Xavi ya tattauna da Messi, Bayern za ta biya Fam miliyan 95 kan Rice

0
156

Tottenham ta dukufa dan hana Manchester United daukar dan wasan Ingila Harry Kane mai shekara 29 a wannan kakar, biyo bayan cijewar shugaban na Spurs Daniel Levy kan sayarda dan wasan ga abokiyar hamayya a Firimiya. (Mirror)

Erik ten Hag ya na ganin zai iya lallabar dan wasan Chelsea da Ingila Mason Mount mai shekara 24 ya koma Manchester United a kokarinsa na gyara wasarsa a kakar bana. (Telegraph)

Bayern Munich ta shirya biyan £95m akan dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, a kokarin kungiyar na buge Arsenal wajen daukar dan kwallon mai shekara 24. (Mirror)

Paris St-Germain ta na so ta yi wuf da dan wasan Arsenal da kuma Norway Martin Odegaard dan shekara 24. (Mail)

Tottenham da Newcastle da kuma Arsenal na daga cikin kungiyoyin Firimiya da ke neman dan wasan Leicester James Maddison, kuma mai shekara 26 din zai iya kaiwa £40m. (Mirror)

Crystal Palace tana neman tsohon shugaban Chelsea da kuma Brighton Graham Potter domin bashi mukamin manaja, a yayin da itama Nice ta ke hangen dan shekara 48 din. (Footmercato – in French)

West Ham ce kan gaba wajen neman dauko James Ward-Prowse, a yayin da Southampton ta shirya bada £40m a kan dan wasan mai shekara 28. (Sun)

Newcastle na ganin za ta dauko dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes mai shekara 25, duk kuwa da son da Barcelona ke yi masa. (90min)

Dan wasan gaba na Brazil mai shekara 31 Roberto Firmino, wanda zai bar Liverpool a kakar bana ya na jiran ya ga inda zai iya shigewa kafun Real Madrid ta dauki mataki kansa (Mail)

Shugaban Barcelona Xavi ya ce ya na tattaunawa da dan wasan Argentina mai shekara 35 kuma mai bugawa Paris St-Germain kwallo Lionel Messi kan yiwuwar komawa Camp Nou. (Standard)

Everton ta na kara kaimi wajen nuna bukatar dauko dan wasan Mali mai shekara 21 El Bilal Toure biyo bayan komawarsa Almeria a ranar Lahadi.(Mail)

Chelsea ta fara tattauna yiwuwar dauko dan wasan Uruguay mai shekara 22 Manuel Ugarte. (90min)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here