Tinubu ya gana da gwamnan babban bankin Najeriya

0
154

Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele a fadar Villa da ke Abuja.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron rantsar da shi, sabon shugaban ya bukaci bankin kasar da yayi dukkan mai yuwuwa wajen daidaita darajar kudin kasar.

Bola Tinubu ya kuma sha alwashin yin garambawul ga sabon tsarin amfani da sabbin kudi da gwamnatin baya ta samar, wanda CBN din ya kaddamar.

“Akwai bukatar a rage kudin ruwa ta yadda za a jawo hankulan masu zuba jari, sannan za a daidaita tsarin kayyade farashin kayayyaki, domin habaka tattalin arzikin Najeriya,” in ji Tinubu.

Wannan ne dai shugaba na uku da Godwin Emefiele zai yi aiki da shi, tun bayan da aka nada shi gwamnan CBN.

Tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya nada Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, haka zalika tshon shugaba Muhammadu Buhari ya bashi damar ya ci gaba da rike mukamin, har zuwa wannan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here