Pochettino ya karbi aikin horar da Chelsea

0
114

Mauricio Pochettino tsohon kociyan Tottenham Hostpur da Paris Saint Germain ya Karbi ragamar horar da Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Ingila a kan kwantiragin shekaru Biyu

 

Pochettino wanda ya fara horar da Celta Vigo ta kasar Spain da kungiyar Southampton Dake Ingila ya shafe shekaru biyar yana horar da Tottenham inda ya kare a mataki na biyu agasar Firimiya a Shekarar 2015 kafin ya kaisu wasan karshe na kofin Zakarun Turai a Shekarar 2019 wanda yayi rashin nasara,daga nan Mauricio ya koma kasar Faransa domin cigaba da aikin horar da Paris Saint Germain

 

A shekaru Biyu da ya shafe a Paris Pochettino ya lashe kofin kalubale na Coupe de France da kuma coupe des Champions abinda ya zama kofuna na farko da ya lashe a shekarun da ya shafe yana horarwa,a Shekarar kuma kungiyar tayi rashin nasarar lashe gasar Ligue 1 bayan karewa na biyu a bayan Lille wacce ta lashe gasar

Mauricio Pochettino ya karbi ragamar horar da Chelsea bayan ta kare a mataki na 12 a gasar Firimiya ta bana mataki mafi kankanta da ta taba karewa a cikin shekaru 25 na baya bayan Nan,Mai Kungiyar Chelsea Todd Boehly yana kyautata zaton Dan kasar Argentina Pochettino zai iya Dawo ma kungiyar martabarta a fagen taka leda

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here