Jagoranci mu ka zo yi ba mulkar ‘yan Nijeriya ba – Tinubu

0
119

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa jagoranci tazo yi ba mulkan ‘yan Nijeriya ba.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Litinin a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Nijeriya na 16.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta dinga yin shawara da tattaunawa ba tilasta wa ba wajen yanke hukunci, don samun kyakkyawar mafita.

“Muna tare da kowa, ba zamu bi son zuciyarmu ba akan ra’ayoyin al’umma.

“Mun zo ne domin mu kara gyara wada kuma warkar da wannan al’umma, ba wai tarwatsa ta da raunata ta ba,” in ji Tinubu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here