Wace kungiya ce za ta iya taka wa Man City burki?

0
112

Kawo yanzu za a iya cewa in dai karfin kungiya ne da buga wasa mai kayatarwa tare kuma da sanin makamar aiki babu kungiyar da za ta iya nuna wa Manchester City karkashin mai koyarwa Pep Guardiola yatsa.

A satin da ya gabata ne tawagar ta Manchester City ta lashe Premier League na bana, bayan da Arsenal ta kasa cin kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest ranar Asabar din da ta gabata.

Nottingham ta yi nasara a filin wasa ta na City Ground da ci 1-0 a wasan mako na 37 a babbar gasar kuma Arsenal wadda take da maki 81 da tazarar maki hudu tsakaninta da Manchester City ta dade tana dakon teburi daga baya aka karbe lokacin da wasannin suka zo karshe.

An fara bude labulen kakar bana da karawar Community Shield, inda Erling Haaland ya yi ta dubi-dubin cin kwallo, yayin da Darwin Nunez ya zura a raga a karawar da Liberpool ta yi nasara cin 3-1.

Nan da nan aka fara surutai kan cewar Haaland ba zai kai labari ba, amma sai ya zura kwallo biyu a wasan farko a Premier League da West Ham sai dai bai ci Bournemouth ba a karawa ta gaba ba, daga nan ya zura a raga a kowacce karawa bakwai da Manchester City ta yi a dukkan fafatawa, har da cin uku rigis sau biyu a jere.

A wasan hamayya Manchester City ta doke Manchester United da cin 6-3 a farkon watan Oktoba kuma dan wasa Haaland ya ci uku a wasan, shima Phil Poden ya zura uku a ragar United.
Wasan ya faranta ran magoya bayan Manchester City, yayin da Manchester United ta buga fafatawar da kwarin gwiwar cewar za ta yi wani abin kirki, bayan samun nasara akan Arsenal da ci 3-1.

Kwallon da ake ganin ta sake taimaka wa Manchester City ita ce wadda dan wasa Kebin de Bruyne ya ci Leicester City, kwallo mai kayatarwa a bugun tazara daga yadi na 25 a filin wasa na King Power.

Amma a karshen watan Oktoba, Haaland ya fara buga dukkanin wasannin Manchester City har ma ya zura kwallo 22 a raga, amma bai yi fafatawar da Manchester City a gidan Leicester ba.

Kungiyar wadda Guardiola yake jagoranta na bukatar cin wasan domin ta koma ta daya a kan teburi, kafin Arsenal ta karbi bakuncin Nottingham Forest a filin was ana Fly Emirates.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka samu bugun tazara daga yadi na 25, kuma Kebin De Bruyne ya dauka ya buga ta kuma fada raga suka hada maki uku kuma daga nan suka ci gaba da matsar Arsenal.

Duk da cewa Arsenal ke jan ragamar teburi, Manchester City ta kwan da sanin kada ta sake barar da maki idan har tana son kamo Arsenal kuma nan da nan Fulham ta tayar da hankalin City ta zura kwallo a raga ta yi kokarin taka mata burkin cin wasa tara a jere a Etihad a dukkan fafatawa.

Sai dai kafin nan minti uku da take wasa Haaland ya ci fenariti, bayan da aka yi wa De Bruyne keta, inda Haaland ya dauki kwallon ya buga ya kuma ci amma duk da haka Manchester City ta sha wahala a wasan, wadda tun a minti na 26 aka bai wa Joao Cancelo jan kati, amma Julian Albarez ya kara ta biyu tun kafin hutu, hakan ya mayar da City kan teburi.

Amma tun bayan da aka kammala wasannin Premier a shekarar 2022, Arsenal tana ta daya a teburi, hakan ya kara nuna cewar akwai jan aiki a gaban City idan har tana son kare kofinta na bara.

Ranar 5 ga watan Janairu City ta ziyarci Chelsea, wadda ta kwan da sanin idan aka doke ta a Stamford Bridge, Arsenal za ta ba ta tazarar maki takwas tsakani sai dai haka aka fara gumurzun ba ci, kuma lokaci na ja, daga nan ne Pep Guardiola ya tashi Jack Grealish da Riyad Mahrez, wadanda ke zaman benci ya saka su a wasan kuma kwalliya ta biya kudin sabulo, domin ‘yan wasan biyu sun taka rawar gani da ta kai Mahrez ya ci kwallo a wasan da aka tashi 1-0.

Wasan da ya canja salon tafiyar Arsenal da Manchester City shi ne na ranar 15 ga watan Fabrairu wanda aka gwada kwazon Arsenal ko za ta iya lashe Premier League na kakar nan, wadda kaka 19 rabonta da shi.

Fafatawa ce tsakanin Arsenal da Manchester City, idan Arsenal ta ci za ta bai wa kungiyar City tazarar maki uku, amma idan City ta yi nasara za ta koma ta daya a kan teburi a karon farko bayan watan Nuwamba.

Dan wasa Bukayo Saka ne ya farke kwallon da De Bruyne ya fara ci, sannan Grealish ya kara ta biyu, wanda ke kan ganiya tun bayan kammala gasar kofin duniya a kasar Katar.
Erling Haaland ne ya zura ta uku a raga, wadanda suka je Emirates kuma a wasan ne ‘yar manuniya ta nuwa Manchester City za ta iya lashe kofin, domin damar hakan na hannunta, bayan kwantan wasa.

Matashin dan wasan baya William Saliba bai sake yi wa Arsenal wasa ba tun bayan da ya ji rauni a karawa da Sporting Lisbon ranar 16 ga watan Maris a gasar Europa League.

Matashin dan wasan Faransan katanga ne a bayan Arsenal kowa ya shaida hakan, amma sai ya ji rauni a Europa League a wasan da Sporting ta cire Arsenal a ranar ta 16 ga watan Maris.

Haka kuma a ranar Arsenal ta rasa mai tsaron baya, Takehiro Tomiyasu, wanda shima har yanzu bai warke ba inda daga nan Arsenal ta yi karawa bakwai kwallo na shiga ragarta a Premier League, in ban da wanda ta ci Newcastle United 2-0 ranar 7 ga watan Mayu, lokacin City ta karbe ragamar teburi.

Wasu daga cikin dalilan da za’a iya cewa su ne suka hana Arsenal lashe firimiya su ne barar da maki a wasan Liberpool bayan da matasan Liberpool suka hana Arsenal damar hada maki uku a filin was ana Anfield a karon farko tun bayan 2012.

Cikin minti 28, Arsenal ta zura kwallo 2-0 a ragar Liberpool, wanda hakan za ta bai wa City tazarar maki takwas tsakani, amma kafin a tashi Liberpool ta farke suka tashi wasa 2-2.

Daga nan ne aka fuskanci kalubalen da ‘yan wasan Arsenal ke ciki a kokarin lashe kofin bana a karon farko tun bayan kakar wasa ta shekarar 2003 zuwa 2004.

Ita kuwa Manchester City sai ta samu damar komai yana hannunta, duk da cewar Arsenal ta bata tazarar maki shida, amma tana da kwantan wasa, sannan Arsenal za ta je gudan ta wato Etihad.

Wani wasa wanda shima ya bayar da gudunmawa wajen hana Arsenal lashe gasar firimiya shine wasan da suka tashi 2-2 da West Ham United domin babu wanda ya yi tunanin Arsenal za ta barar da maki a sauran wasannin da ke gabanta, bayan yin 2-2 da Liverpool.

Gabriel Jesus da Martin Odegaard ne suka ci West Ham kwallaye 2-0, bayan minti 10, amma daga baya Said Benrahma ya farke a minti na 33 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan Jarrod Bowen ya farke a minti na 54 kuma hakan ya sa wasa na biyu a jere da Arsenal ta tashi 2-2 kenan a Premier, bayan wanda ta yi a gidan Liberpool.

Kawo yanzu dai za’a iya cewa Arsenal tayi kokari ganin manyan kungiyoyin da suke gasar firimiya da suka hada da Chelsea da Liberpool da Manchester United da kuma Newcastle United amma sun kasa kokarin takawa Manchester City burki.

Yanzu dai abinda ya rage shine jiran irin gyaran da Arsenal za tayi ta hanyar sayan manyan ‘yan wasan da zasu taimakawa kungiyar wajen jure wahalar lashe firimiya kamar yadda Manchester City take da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here