Madrid za ta dauki Bellingham, Rice na hangen Arsenal

0
114

Real Madrid za ta dauki dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19 daga Borussia Dortmund a mako mai zuwa. (Marca – in Spanish)

Dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, ya fi son ya koma Arsenal a kakar wasa ta bana a yayin da Manchester United da Chelsea da kuma Bayern Munich duk ke zawarcin dan kwallon mai shekara 24. (Mirror)

Har yanzu kudin da Manchester United ta taya Mason Mount, ba su kai £55m da Chelsea ke bukata ba duk kuwa da kasancewarta kan gaba daga cikin wadanda suka taya dan wasan mai shekara 24. (Independent)

Chelsea za ta sayar da daya daga cikin masu tsare mata raga inda ake sa ran dan kasar Senegal Edouard Mendy, mai shekara 31 zai barta. (90min)

Newcastle ta aike da mutanenta har sau biyu domin sa ido a kan dan wasan tsakiya na kungiyar RB Leipzig da kuma Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 22 a daren Jumma’a. (Sky Sports)

Manchester City ta kebe euro miliyan 40 domin dan wasan Portugal Joao Cancelo, wanda ya ke yiwa Bayern Munich wasa a halin yanzu, a yayin da itama Barcelona ke zawarcin dan wasan mai shekara 28. (Sport – in Spanish)

City ta shirya yin musayar Cancelo da dan wasan Bayern da kuma Jamus Joshua Kimmich, mai shekara 28. (90min)

Marco Asensio ya shirya barin Real Madrid idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar bana a yayin da ya gaza cimma matsaya da kungiyar. (Athletic – subscription required)

Asensio na duba yiwuwar komawa Paris St-Germain bayan karewar kwantiraginsa. (ESPN)

Tottenham na kan gaba wajen neman mai tsaron ragar Brentford da kuma Spaniya David Raya, dan shekara 27. (GiveMesport)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here