Gayyatar da El-Rufai ya yi wa Kwankwaso da wacce Abba ya yi wa Muhammadu Sanusi II sun janyo muhawara

0
177

Gayyatar da gwamnan Jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya, Malam Nasir El-Rufai, ya yi wa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, don kaddamar da wasu ayyuka a jiharsa ta sa ana tafka muhawara game da muhimmancin yin siyasar akida.

Ranar Juma’a Gwamna El-Rufai, wanda fitaccen gwamna ne a jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, ya gayyaci wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da Sanata Kwankwaso don bude tarin ayyukan da gwamnatinsa ta yi.

Sai dai babban abin da ya fi jan hankalin ‘yan Nijeriya, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, shi ne gayyatar da gwamnan ya yi wa Sanata Kwankwaso don kaddamar da kasuwar Ungwan Rimi da Emir Road da kuma School Road.

Kwankwaso ya yi takarar shugaban Nijeriya a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar NNPP, wadda ta sha kaye a hannun jam’iyyar APC.

Hotunan da suka watsu a shafukan sada zumunta sun nuna Gwamna El-Rufai cikin murmushi rike da na’urar magana yayin da shi kuma Sanata Kwankwaso ya rike almakashin da ake yanka kyallen da ke nuna alamar kaddamar da ayyuka.

Sanata Kwankwaso ya jinjina wa Gwamna El-Rufai, wanda ya bayyana a matsayin “dan uwana”, bisa ayyukan da ya yi domin ci-gaban al’ummarsa.

Kwankwaso ya kaddamar da wadannan ayyuka ne kwana guda bayan gwamnatin Neja ta gayyace shi domin yin lacca a wurin taron kaddamar da zababben gwamnan jihar Mohammed Umar Bego na jam’iyyar APC.

Kazalika dukkan wadannan abubuwa na faruwa ne mako kadan bayan tsohon gwamnan na Kano ya gana da zababben shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, a birnin Paris, abin da ake gani a matsayin wani mataki na komawarsa jam’iyyar APC.

Sai dai fitaccen dan siyasar ya shaida wa TRT Afrika cewa nan ba da jimawa ba zai yi bayani game da dalilin ganawarsa da Bola Tinubu.

‘Daraja daga Allah’

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum da masu fada a ji a shafukan zumunta na ganin darajar Sanata Kwankwaso ce take karuwa shi ya sa ‘yan jam’iyyun hamayya suke gayyatarsa don kaddamar da ayyukan da suka yi.

Wasu kuma na cewa ya kamata irin wannan mataki ya zama izina ga masu fada kan ‘yan siyasa don su farga cewa babu rashin jituwa ta dindindin a siyasa.

Wani fitaccen mai sharhi a shafukan zumunta, Dr Ibrahim Musa, ya ce gayyatar da Gwamna El-Rufai ya yi wa Sanata Kwankwaso na nuna muhibbarsa yana mai yi masa addu’a “Allah ya kara daraja, jagora nagari.”

Shi kuwa Malam Muhsin Ibrahim cewa ya yi “Na daɗe ina cewa ƴan siyasar Najeriya sun fi kusa da junansu sama da yadda muke zato. Shi ya sa shirme ne faɗa da abokinka, ko maƙocinka kai wasu ma har da ƴanuwansu (!) saboda su.”

Muhsin ya nemi masu fada kan ‘yan siyasa su yi taka-tsantsan. Hoto/Muhsin Ibrahim Facebook

Sai dai kafin a kammala muhawara kan wannan batu, sai wata takardar gayyata da zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zuwa bikin rantsar da shi ta bulla a shafukan zumunta.

A 2020 aka cire Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano. Hoto/Abba Kabir Yusuf

“Ina gayyatarka bikin rantsar da ni da mataimakina Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo. Zuwanka wajen bikin zai kasance muhimmin ci-gaba da goyon baya a gare mu,” in ji takardar gayyatar.

A watan Maris na shekarar 2020 ne Gwamna Abdullahi Ganduje, mai barin gado, ya cire Muhammadu Sanusi II daga kan sarauta bisa zarginsa da saba wa dokokin aiki, zargin da tsohon sarkin ya musanta.

Kuma tun bayan yin nasara a zaben gwamnan Kano, ake rade-radin zababben gwamnan jihar zai dawo da tsohon sarkin kan sarauta, ko da yake tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, ya ce sabon gwamna ne kadai zai yanke shawarar daukar mataki kan lamarin.

Masu sharhi na ganin gayyatar ta sake tado da rade-radin da ake yi game da yiwuwar dawo da tsohon sarki, abin da wani Malam Muhammadu Inuwa II ya ce yana daure masa kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here