Ganduje ya rantsar da sabon kwamishina ’yan sa’o’i kafin ya bar mulki

0
124

Yayin da ya rage ’yan sa’o’i ya bar mulki, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Juma’a ya rantsar da sabon Kwamishina.

Rantsuwar na zuwa ne kasa da mako daya bayan Gwamnan ya ba dukkan masu rike da mukaman siyasa a Jihar umarnin su ajiye mukamansu zuwa ranar Juma’a.

Ganduje dai ya rantsar Abdullahi Abba Sumaila ne a matsayin sabon Kwamishina a Hukumar Zabe ta Jihar (KANSIEC).

Kwamishinan Shari’a na Jihar mai barin gado, Barista M A Lawan ne ya rantsar da sabon kwamishinan yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar na karshe wanda ya gudana daren Juma’a a Fadar Gwamnatin Kano.

Da yake jawabi bayan rantsar da sabon Kwamishinan Gwamna Ganduje ya ce an rantsar da Kwamishinan ne bayan Majalisar Dokokin Jihar kano ta tantance tare da Amincewa da nada shi a matsayin.

“Muna fatan zaka yi aikin ka yadda ya dace saboda muhimmancin da hukumar zabe take da shi musamman wajen shirya zaben Kananan Hukumomi a jihar Kano.” in ji Ganduje

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here