Hukumar aikin Hajji ta lashe amanta kan karin kudi

0
116

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta lashe amanta bayan alkawarin da ta yi cewa maniyyatan Najeriya ba za su biya karin Dala 250 da aka samu kan kudin kujerar Hajjin bana daga aljihunsu ba.

Sabanin alkawari da tabbacin da hukumar ta ba wa maniyyatan a baya, a ranar Litinin ta sanar da cewa yanzu za su biya cikon Dala 100.

Shugaban NAHCON, Hassan Zikrullahi, ta hannun Mataimakin Daraktan Yada Labaran hukumar, Mousa Ubandawaki, ya ce, karin Dala 100 maniyyatan za su biya daga cikin karin Dala 250 da aka samu, a yayin da gwamnati da kamfanoni jirage kuma sauki dauki alhakin cikon.

Ubandawaki ya ce bayan karin Dala 250 da aka samu, gwamnati ta yafe musu Dala 55, wanda ya sa kudin kujerar ya ragu zuwa Dala 195.

“Yanzu kowane mutum daga cikin maniyyatan su 75,000 zai biya cikon Dala 117,” in ji Ubandawaki.

Amma ya bayyana cewa maimakon maniyyata su biya wani kudi daga alhjihunsu, Hukumar za ta cire Dala 100 daga kudin guzurinsu a matsayin cikon kudin kujerar, sai a ba su Dala 700 a matsayin kudin guzuri.

Ya ce cikon Dala 17 kuma NAHCON ta roki kamfanonin jirage su yi wa maniyyatan rangwame, saboda su ma ba yin su ba ne mastalar da ta sa aka rufe sararin samaniyar kasar Sudan.

Amma ya kara da cewa idan har aka bude sararin samaniyar Sudan kafin fara jigilar maniyyata, to za a mayar musu da kudensu da aka cira.

Yakin da ya barke a Sudan ya sa aka hana shawagin jirage a sararin samaniyar kasar, inda kuma ta nan jiragen alhazan Najeriya suka saba bi zuwa kasar Saudiyya.

Rufe sararin samaniyar Sudan ya sa dole sai jiragen sun sauya hanya, wanda zai kara yawan sa’o’in da za su dauka, da kuma yawan kasashe da za su bi kafin isa Saudiyya.

A kan haka ne kamfanonin jiragen jigilar maniyyatan Najeriya suka nemi karin Dala 500 a kan kudin kowace kujera, amma a karshe suka daidaita da NAHCON a kan Dala 250.

Da farko NAHCON ta ce za ta yi bakin kokarin ganin maniyyatan ba za su biya karin daga aljihunsu ba.

Amma daga bisani ta fito da wannan sanarwa da ke cewa gwamnati ta biya musu wani bangare, za su biya Dala 100, wanda za a cira daga kudin guzurinsu, maimakon su yi ciko; kamfanonin jirage kuma za su yi musu ragin Dala 17.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here