Wadanne abubuwa za a fi tuna Shugaba Buhari da su?

0
113

Idan ya sauka daga kan mulki a mako mai zuwa, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya ne cikin matsalar tsaro da talauci da kuma karin bashi fiye da yadda ya karbi kasar a 2015.

Tsohon shugaban a mulkin soji ya zama shugaban kasa bayan da ya lashe zabe da ya kai ga karshen mulkin Goodluck Jonathan wanda ya gaza a bangarori da dama.

Kasancewar yana tafiya ne kan fatan cewa sauyi abu ne mai yiwuwa, ya samu goyon bayan hadaka mai karfi sannan ya yi fice a matsayinsa na soja mai aiwatar da ayyuka.

Bayan wa’adin mulkin Buhari a shekarun 1980, ya dawo a karo na biyu da alkawarin magance matsalar ta’addanci a yankin arewa maso gabas da kuma magance cin hanci da rashawa.

Shi ne na karshe cikin jerin sojoji da Birtaniya ta ba su horo da suka mulki kasar.

Sai dai mulkin shugaban mai shekara 80 ya jefa mutane da dama cikin takaici.

An samu nasara wajen magance Boko Haram da wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi a arewa maso gabas, bisa taimakon makaman yaki daga Amurka.

Yayin da kungiyoyi ke ci gaba da kai hare-hare kan yankuna da sansanin jami’an tsaro a yankin, an samu gagarumin ci gaba daga shekarun baya a lokacin da suke cin karensu ba babbaka har suke rike da wasu wurare da dama na yankunan Najeriya.

Buhari ya kuma yi amfani da basukan China wajen inganta titi da layin dogo, ya kuma gina sabuwar tashar ruwa a Legas da kammala muhimmiyar gada a kudu maso gabas tare da amincewa da dokokin zabe da na bangaren mai.

Amma duk nasarorin da aka samu a arewa maso gabas game da masu ikirarin jihadi sun shafe saboda bullar wasu miyagun kungiyoyin a wasu sassan kasar a karkashin mulkinsa.

Tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma da ya jima yana faruwa, an kyale shi yana ruruwa har ta kai ga amfani da makamai da kuma kabilanci yayin da gwamnati ta rasa hanyoyin nemo mafita ga masu kiwo.

Ana zargin Buhari, wanda Fulani ne daga Arewacin Najeriya, da nuna son kai a rikicin kuma shawararsa ta samar da wuraren kiwo ga manoman ba ta samu goyon bayan gwamnonin jihohin kudanci ba wanda ke ganin hakan a matsayin wata dabara ta kwace iko da filinsu.

Wasu kungiyoyi masu rike da makamai da rikicin makiyaya da manoma ya haifar tuni suka rikide suka zama yan bindiga da ke kai hare-hare kan babura a arewa maso yamma da tsakiyar kasar.

Wadannan kungiyoyin sun taimaka wajen mayar da sace mutane don neman kudin fansa a matsayin wata gwaggwabar sana’a da ta yadu zuwa sassan kasar.

Ya faru ne a shekara 10 na farkon karnin nan lokacin da aka sace ma’aikatan mai a yankin Neja Delta, ya kuma girmama a karkashin ikon Buhari.

Misali, an sace dubban kananan yara ‘yan makaranta tsakanin Disamban 2020 da Satumban 2021, a cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef. An kuma sace dalibai mata 270 daga makarantarsu a Chibok labarin da ya karade kafafen yada labarai na duniya a 2014 – wani laifi da ya zama babban dalilin nasarar da Buhari ya samu a kan Jonathan.

“Na yi tunanin a matsayinsa na tsohon shugaba a mulkin soji, yana da maganin matsalolin tsaron Najeriya,” in ji Musa Ahmadu wani manoma da ke zaune a jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasa.

Ahmad, wanda ya fito daga jihar Shugaban kasa wato Katsina, ya bar garinsa zuwa Kano tare da dubban mutane saboda ayyukan yan bindiga a yankin.

Mutane da dama suma suna ganin Buhari, ya yi kuskure a yadda ya tafiyar da batun jagoran yan aware na Ipob, Nnamdi Kanu.

Ipob na neman ballewa daga Najeriya wadda kuma gwamnati ta haramta ta.

Yan Najeriya da dama sun yi watsi da Ipob har sai da gwamnatin Buhari ta kama Kanu kan zargin cin amanar kasa a 2015. Wani hari da aka kai kan gidansa ya zama mafarin fito na fito da ta wuce gona da iri, lamarin da ya janyo mutuwar daruruwan mutane.

Bayan ya tsere a 2017, an kama shi tare da tisa keyarsa zuwa gida Najeriya a 2021 domin fuskantar shari’a. Wani alkali ya bayar da umarnin a sake shi saboda tsarin da aka bi na mayar da shi Najeriya ba ya bisa doka sai dai hukumomi sun ci gaba da rike shi.

Wadannan kalubalen tsaro sun sa mutane da yawa nuna shakku kan yadda Buhari yake tafiyar da batun da ya kamata a ce ya nuna kwarewa a kai.

“Na yi mamakin irin abin kunyar da ya janyo ga sojoji, duk da alkawuran da ya dauka,” in ji tsohon soja Kanar Hassan Stan-Labi, wani mai sharhi kan sha’anin tsaro.

“Ta ya za ka gaza a angaren da ka fi karfi? ya tambaya.

Matsalar tsaron a fadin kasar karkashin Buhari ta lafa a yankin Neja Delta mai arzikin mai inda barayin mai suke cin karensu ba babbaka a baya.

Sai dai zaman lafiyar da aka gani da alama ya yi daidai da lokacin da ake ganin sace-sacen mai inda ake zargin gwamnati da kawar da kai yayin da kungiyoyi da dama a yankin ke wawushe danyen mai daga bututai. Hakan ya sa man da Najeriya ke samarwa yin kasa a 2022.

Masu sharhi sun bayyana gano wani dogon bututu a watan Oktoban bara da ake amfani da shi wajen sace danyen mai a matsayin abin da ba lallai ya yiwu ba ba tare da taimakon hukumomi ba.

A wani waje, barayi sun gina nasu bututun mai tsawon kilomita 4 zuwa tekun atalantika. A nan, jiragen ruwa suna dakon man da aka sato.

Irin wannan satar da ake yi na faruwa ne a karkashin mulkin Buhari, wanda kuma ya kasance ministan man fetur, ta yi zagon kasa ga ikirarinsa na yakar cin hanci, in ji Salaudeen Hashim na wata kungiya mai zaman kanta Cleen Foundation da ke yakar cin hanci.

Nagartar Buhari ta disashe saboda yawan tafiye-tafiyensa na neman magani zuwa Birtaniya duk da kashe makudan kudi wajen gyara asibitin Fadar Shugaban kasa.

Wannan rashin nuna gaskiya “ya kwashe kudaden masu haraji, ya karfafa safarar kudi ta haramtacciyar hanya da sauran ayyukan cin hanci da rashawa da gwamnatin ta yi suka a kai,” kamar yadda shugaban kungiyar Transparency International a Najeriya, Auwal Rafsanjani ya fada wa BBC.

Rafsanjani ya bai wa gwamnatin maki hudu cikin 10 a yaki da cin hanci inda kuma ya ce nadin mutanen da ake zargi da cin hanci da Buhari ya nada a gwamnatinsa da kuma zaman mai dakinsa na tsawon lokaci a Dubai ” sun saba da nagartattun ayyukan gwamnatin da ke yaki da cin hanci da wadaka da kudi.”

Yayin da yake yin bankwana da mulki, za a rika tunawa da yadda Buhari ke tafiyar da tattalin arzikin Najeriya saboda yunkurinsa a farkon shekarar nan na sauya fasalin takardun kudin kasar.

Lamarin da ya jefa kasar cikin rudani yayin da karancin sabbin takardun naira da a yanzu sun bace, ya jefa miliyoyin yan kasar cikin mawuyacin hali musamman kasancewar sun raja’a kan takardun kudin wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

“Karamar sana’ar da muke, mutumin nan ya durkusar da ita,” in ji wata daliba da ta kammala jami’a a Abuja wadda take samun kudi ta hanyar samar da takardun kudi ga abokan huldarta kafin a shiga matsalar karancin kudin.

Matsalar da ake fama da ita a Najeriya ne ya fusata ta – rashin aiki a tsakanin matasa masu ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here