El-Rufai ya tube sarakunan Piriga da Arak

0
107

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amince da tsige sarakunan Piriga da Arak, Mai Martaba Jonathan Paragua Zamuna, da Mai Martaba Janar Aliyu Iliyah Yammah (Mai ritaya)

Kwamishiniyar Al’amuran kananan Hukumomin Jihar, Hajiya Umma Ahmad, ce ta bayyana tsige Sarakunan biyu cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin, inda ta ce sarakunan biyu sun daina gudanar da ofisoshinsu daga ranar Litinin 22 ga watan Mayun 2023.

Kwamishinan ta kara da cewa matakin tsige sun ya biyo bayan shawarwarin da ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta yi bisa tanadin sashe na 11 na dokar da ta shafi sarautu mai lamba 21 ta shekarar 2021.

A cewar ta, “Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, shi ne zai kula da al’amuran masarautar Piriga, har zuwa lokacin da za a nada sabon sarki, yayin da aka umarci sakataren majalisar da ya fara aikin nadin sabon Hakimin.

“Sakataren majalisar masarautar Arak, shi ne zai kula da al’amuran masarautar tare da kaddamar da tsarin nada sabon sarki.”

Sanarwar ta kara da cewa, “gwamnati ta ga yadda martanin da Janar Iliyah Yammah ya bayar game da batun nadin hakimai hudu, sabanin wanda aka amince da shi a masarautarsa, da rashin zama a masarautar Arak.

“Tsige Sarki Jonathan Zamuna ya biyo bayan rikicin kabilanci da ya barke tsakanin al’ummar Gure da Kitimi na Piriga a karamar hukumar Lere, da rashin zama a cikin masarautar.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here