Gwamnatin Buhari ta kashe sama da dala biliyan 7 a bunkasa wutar lantarki-Bincike

0
131

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kashe sama da Dala biliyan 7.5 da ta ciyo bashi wajen bunkasa hasken wutar lantarki a kasar, amma har yanzu ana fama da duhu.

Jaridar The Guardian da ake wallafawa a kasar a binciken da ta gudanar ta gano an ciyo bashin makudan kudin ne da zummar gyaran dukkanin matsalar da ake fuskanta a bangaren samar da hasken lantarkin don samar da wadatar ta ga daukacin sassan kasar, sai dai ana iya cewa hakan ya kare a hasashe.

A cewar jaridar, gwamnatin Buhari ta karbo basukan ne daga Bankin duniya, Bankin raya kasashen Afirka da kuma hukumar raya kasashen Faransa da Japan da dai makamantan su. Saboda gudanar da aiyukan bunkasar bangaren samar da hasken lantarkin, amma wasu dalilai sun hana cimma wannan buri.

Ana zargin batutuwan rashawa, alfarmar siyasa da rashin gamsashen tsari na bangarorin dake da ruwa da tsaki a harkar samar da hasken lantarkin na daga cikin dalilan da suka haifar da tsaiko wajen gudanar da aiyukan da suka dace har ya sanya aka karbo basussukan kuma hakar ta kasa cimma ruwa. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here