Shugaban EFCC ya nemi cin hancin $2m a wajena, ina da hujja – Matawalle

0
95

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya zargi shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya nemi ya ba shi toshiyar baki na Dala miliyan biyu.

Matawalle wanda ke cikin jerin wadanda EFCC ke zargi da badalalar biliyan 70 a halin yanzu, ya nuna cewa Bawa ya bukaci ya ba shi cin hancin amma da ya ki sai ya tasosa gaba.

“Bincike gaskiya ne, ba a hana a yi bincike ba, amma kuma ya kamata binciken ya zamo na kowa da kowa, don bai kamata a ce komai sai dai a ambaci gwamna ba, ai ba gwamna ne kadai ke da asusun ajiya ba.”

“Kamar yadda shugaban EFCC ya ce ya tanadi takardu na gwamnoni, to muna so ya nuna wa duniya takardu na wadanda yake aiki tare da su, sannan shi kansa ya kamata ya rubuta wa kansa takarda don a bincike shi saboda akwai zarge-zarge masu dumbin yawa a kansa,” A cewar Matawalle.

A hirarsa da BBC Hausa da wakilinmu ya bibiya, Matawalle ya kalubalanci Bawa da ya sauka daga kan kujerarsa ya bayar da damar a bincike shi ya ga irin abubuwan da za a bankado.

Gwamnan na Zamfara, ya ce “Akwai shaidu da dama wadanda idan ya sauka za a fito da su a gwada wa duniya cewa shi ba mai gaskiya ba ne. Ya sauka ya gani duk wadanda ke da wata shaida a kansa za su kawo a cikin lokaci kalilan.”

Gwamna Matawalle, ya kara da cewa “Akwai abin da shi shugaban EFCC ya san ya yi tsakaninsa da ni, ya san abin da ya roka ban ba shi ba a kan haka ya sani gaba.”

Sai dai ita ma hukumar ta EFCC ta kalubalanci gwamnan jihar Zamfarar, Bello Matawalle kan cewa idan yana da hujja a kan cewar shugabanta, Abdulrasheed Bawa na da hannu a ayyukan rashawa to ya kai kara wajen ‘yan sanda.

Da aka tuntubi shugaban hukumar, Malam Abdulrasheed Bawa, ya ce ai babu wani dan adama da yake 100 bisa 100 a duniya.

Ya ce, “Amma dai gwargwadon hali wadannan maganganu da gwamna Matawalle yake yi, wane ya yi kaza, ai sai ya fadi.”

Shugaban na EFCC ya ce, ‘’Idan ya san akwai wani gwamna ko minista da ya yi wani abu ya zo ya kawo, idan kuma ya ga cewa ni na yi wani abu ai akwai ‘yan sanda da wuraren da zai iya rubuta kara sai ya kai idan ya so sai a bincike ni, in ya so sai a gano wanda ke da gaskiya.”

An dai shiga takun saka tsakanin gwamnan da EFCC ne bayan da hukumar ta ce ta aike da goron gayyata ga wasu gwamnoni da za su sauka a karshen watannan domin ta bincike su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here