Masana: Hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka zai sa a samu sabuwar damar zamanantar da nahiyar Afirka

0
117

An gudanar da babban taron tattaunawa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fannin wayar da kai karo na 2 mai taken “zamanantarwa irin ta kasar Sin da hanyar raya Afirka” daga ranar 16 zuwa 17 ga watan a birnin Beijing. Wasu masana suna ganin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kawo sabuwar dama ga bunkasuwa da zamanintar da nahiyar Afirka.

Daraktan cibiyar nazarin harkokin Sin ta Najeriya, Charles Onunaiju, ya bayyana a cikin jawabin da ya gabatar a kan karamin dandalin tattaunawar cewa, neman gaskiya da hada ka’ida tare da gaskiya, shi ne darasin samun nasara a cikin zamanintarwa irin ta kasar Sin. Ya ce kasar Sin ce abokiyar kasashen Afirka dake da tunani da kwarewa wajen ba da taimako kan bunkasuwar su, wadda ba kasafai a kan sami irinta ba.

A nasa bangaren shugaban kwalejin nazarin Sin da kasashen Afirka na jami’ar Makeni dake Saliyo, Alpha Mohamed Jalloh, ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kawo babban damammaki ga nahiyar Afirka, a sa’i daya kuma yana fatan cewa, hadin gwiwarsu na iya habaka zuwa wasu fannoni, ba kawai a fannonin raya tattalin arziki da gina manyan ababen more rayuwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here