Ana rige-rigen siyan Sadio Mane, United ta kammala shirin dauko Adrien Rabiot

0
95

Manchester United da Newcastle United na rige-rigen dauko Sadio Mane daga kungiyar sa ta Bayern Munich bayan da ya kasa yin katabus a gasar Bundesliga ta Jamus. (Mail)

Kungiyoyin Chelsea da Manchester United da Tottenham da kuma Fulham na daga cikin kungiyoyin kwallon kafar da ke sha’awar dauko dan wasan Najeriya Gift Orban, mai shekara 20. (Evening Standard)

Manchester United ta kammala shirye-shiryen ta na dauko dan wasan tsakiya na Juventus da Faransa Adrien Rabiot, mai shekaru 28 da Kim Min-jae mai shekara 26 da ke taka leda a Napoli . (Mirror)

Ita kuwa Brighton na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister mai shakara 24, sa’anan Liverpool na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Ingila kuma dan wasan Chelsea Mason Mount. Haka ma Bayern Munich na duba yiwuwar sayo dan wasan tsakiyar Netherland Ryan Gravenberch mai shekara 21. (Liverpool Echo)

Liverpool ta nuna sha‘awar sayo dan wasan Feyenoord da Turkiya Orkun Kokcu, mai shakara 22 kuma ana iya maye gurbin Mac Allister ko dan wasan tsakiyar Dortmund Jude Bellingham 19. (Football Transfer)

Manchester City na shirin dauko dan wasan baya na RB Leipzig da Croatia Josko Gvardiol a yayin da kungiyar Jamus ta bukaci fam miliyan 85 ga dan wasan mai shekaru 21. Leipzig ke naman pan £85m kann dan shakara 21. (Mail)

AC Milan na shirin dauko dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Ruben Loftus-Cheek mai shekara 27, tun bayan da suka kasa yin katabus a gasar zakarun Turai inda suka sha kayi a wasan kusa da na karshe a hannun Inter Milan. (Fabrizio Romano on Twitter)

Tottenham ta fara tattaunawa da manajan kungiyar Feyenoord ta Netherlands don yiwuwar bashi aikin horar da kungiyar. (Football Insider)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here