Zan kai gwamnatin Buhari ƙara idan ta ci bashin dala miliyan 800-Ndume

0
109

Dan Majalisar Dattijai mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume ya yi barazanar kai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kotu idan ta karbo rancen dala miliyan 800.

A farkon watan Mayu ne shugaban ya aika wa majalisar dattawan ƙasar wata takarda da ke neman majalisar ta amince masa karɓo bashin kudin daga bankin duniya domin rage raɗaɗin da za a sha sanadin cire tallafin mai.

Hakan na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi cikin watan Afirilu na bayar da tallafin dala miliyan 800 na bankin duniya ga ƴan Najeriya masu rauni su miliyan 50 ko gidaje miliyan 10.

Wannan batun dai ya janyo zazzafar muhawara kuma Sanata Ndume na cikin masu sukar matakin.

Dan majalisar ya ce ya kamata a ci bashi ne don a yi wa mutane abin da zai amfane su.

Dan majalisar ya ce kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba, saboda idan aka raba wa mutum miliyan 50 kudin abin da mutum daya zai samu ba zai wuci naira 7,200 bisa la’akari da canjin dala.

“Idan za a ci bashin a bai wa kananan hukumomi su yi ayyukan da al’umma za su ci moriyarsu to da sauki, amma ni ba na goyon bayan a ciwo bashi sannan a cinye.

Yadda aka zabi wadanda za su ci moriyar kudin da kuma cewa dukkan ‘yan Najeriya ne za su biya abu ne da ya sabawa kundin dokar Naajeriya” a cewar Sanata Ndume.

Har’ilayau, dan majalisar ya ce ba ya goyon bayan a ciwo bashi sannan wasu mutanen daban su cinye a bar gwamnati da biya.

Ya kuma kara da cewa ko da Shugaba Buhari ne ya saurari bayaninsa zai iya fada mishi ya je kotu kan batun.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce za a rarraba tallafin ne don rage wa mutane wahalar da za su iya shiga idan aka cire tallafin mai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here