Home Labarai Wasanni Aubameyang ya janye matakinsa na ritaya daga dokawa Gabon kwallo

Aubameyang ya janye matakinsa na ritaya daga dokawa Gabon kwallo

0
100

Aubameyang dan Gabon mai shekaru 33 da ke matsayin mafi zurawa kasarsa kwallo, a watan Mayun shekarar 2022 ne ya sanar da ritaya daga kwallo amma kuma a jiya ya shaidawa manema labarai aniyarsa ta dawowa ci gaba da dokawa kasar kwallo.

Dan wasan na Gabon da ya zura kwallaye 28 a wasanni 68 da ya dokawa kasarsa, ya ce ya dauki matakin ne bayan ganawa da shugaban kasar Ali Bongo Ondimba da ya bukace shi da ya koma cikin tawagar.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Auba ya ce zai koma dokawa Gabon wasa dai dai lokacin da kasar ke jagorancin teburinta a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika.

Komawar Aubameyang cikin tawagar ta Gabon dai zai sake karfafata wanda ke nuna yiwuwar ta samu gurbi a gasar da ta gudana cikin watan Janairun badi a Ivory Coast.

Aubameyang haifaffen Faransa da yanzu haka ke taka leda da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea wadda ta sayo shi daga Barcelona ana ganin matakin Arsenal na bashi mukamin kyaftin a shekarar 2021 ne ya sanya shi a zafin da ya kai shi ga daukar matakin daina takawa kasar ta shi leda.

Akwai dai jita-jitar da ke alakanta Aubameyang da yiwa Barcelona kome a kakar wasa mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here