Dalilin da ya sa na nemi mazajen da na aura su sake ni — Laila Othman

0
131

’Yar kasuwa kuma fitacciya a dandalin sada zumunta Laila Ali Othman ta ce dalilin da aure biyu da ta yi a baya suka mutu shi ne da saboda ta yi wa rayuwar kallon kitsen rogo.

Laila ta bayyana hakan ne a tattaunawarta da Sashin Hausa na BBC kan halin da mata ke shiga a kasar Hausa bayan mutuwar aurensu.

Ta kuma ce lokacin da aurenta na biyu ya mutu babu wanda ya tallafa mata daga danginta ko kawaye ko wani a waje, duk wata nasara da ta samu a yanzu, ta same ta ne ta hanyar jajircewa.

“Lokacin da na rabu da mijina na biyu, zan iya cewa babu mutum daya da ya tallafa min, ba ’yan uwa ba, ba kawaye ba.

“Saboda ni tunda na tashi agidanmu, kowa na min kallon fitinanniyar yarinya mai aikata abin da nake so a lokacin da na so; Wannan ya sa ake ganin ni na kori mijin, na sa ya rabu da ni.

“Kuma maganar gaskiya haka ne, duk aure na biyu da na yi ni ce na ce ina so na rabu da mijin, kuma ba don mijin ya yi min wani abu da ya saba wa na yau da kullum ba —kawai ka auri mutum kana ganin rayuwar da ka yi tunanin ita ce sai ka taras ba ita ce ba.

“Sannan zama da shi zai ci gaba da kawo min zunubi, saboda zan iya zuwa ina ta yi masa bakin rai, ko na ki dafa masa abinci, ko duk wani abu da ya kamata a matsayinki na mace ki yi wa namiji, na ce ba zan yi ba.

“Don haka gara a ce ba na gidan da na ci gaba da neman zunubi,” in ji ta.

Haka kuma ta ce surutun mutane kan mutuwar auren nata bai taba damun ta ba, saboda a ganinta ana yin aure ne don gamsuwar kai da bin umarnin Allah, ba don abin da wani zai ce ba.

Ta ce mutuwar aure ga mata ba lokaci ne na samun sauki ko jin dadi ba, lokaci ne na jajircewada hakuri da komawa ga Allah don samun nasara, domin ta haka ne kadai wadanda suka guje ta a baya za su dawo gare ta.

Sai dai ta shawarci matan da ke da aniyar ficewa daga gidajen aurensu, da su tabbatar za su yi ne don samun ci gaban rayuwarsu, ba don yawon banza ko tunanin za su samu mijin da ya fi wanda za su rabu da shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here