Abubuwan da ake koya wa sabbin gwamnonin Najeriya a taron horar da su

0
117

A ranar Litinin 29 ga watan Mayun nan ne za a rantsar da sababbin gwamnonin Nijeriya na jihohi 18.

Gabanin hakan ne Kungiyar Gwamnoni ta Nijeriya NGF ta shirya wani taron horar da sababbin gwamnonin da ma masu yin ta-zarce, a Abuja, babban birnin Nijeriya.

A ranar 11 ga watan Maris na 2023 ne aka gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 31 daga cikin 36 na kasar, sai dai kuma 18 daga cikin su ne kawai sababbin gwamnoni a karon farko, yayin da sauran 13 ta-zarce suka yi.

Mece ce manufar taron? Su waye mahalartansa? Me ake horar da gwamnonin?

Wadannan su ne tambayoyin da wannan makala za ta duba amsoshinsu.

Mece ce manufar taron?

Mai magana da yawun Kungiyar NGF Abdulrazaque Barkindo ya shaida wa TRT Afirka cewa dama al’adar kungiyar ce shirya irin wannan taro na horarwa a duk lokacin da za a rantsar da sababbin gwamnoni.

Sababbin gwamnoni ‘yan karon farko 18 ake da su sai kuma 13 da suka yi ta-zarce/Hoto: NGF

Sauran abubuwan da ya bayyana a matsayin manufar taron su ne:

  • Yi wa sababbin gwamnoni maraba
  • Yi musu bayani kan irin ayyukan da ke gabansu da bukatun al’umma da ke rataye a wuyansu
  • Dora su a gwadaben tafiyar da gwamnati fiye da yadda aka gudanar da yakin neman zabe
  • Horar da su kan sahihan hanyoyin tafiyar da gwamnati
  • Yi musu jawabai kan yadda za su zabi kwararrun ma’aikatan da ya kamata su dauka wajen tafiyar da mulki don inganta rayuwar al’umma
  • Yadda ya kamata su yi la’akari da kwarewar kowa yayin zabar masu taimaka musu don sanya kowa a gurbin da ya dace
  • Yadda za su fahimci manyan bukatun al’umma da suka kamata su bai wa fifiko tun farkon fara mulki.

Karfafa zuciyoyin gwamnoni masu barin gado

Baya ga shirya sababbin gwamnoni kan yadda za su durfafi mulki, daga cikin manyan manufofin taron kuma har da mayar da hankali kan bai wa gwamnonin da wa’adinsu ya kare shawarwari na yadda za su durfafi rayuwa bayan barin mulki.

“Daga cikin manufofin taron har da yi wa gwamnoni masu barin gado gargadi da kuma nuna musu cewa ko da bayan sun bar mulki, to suna da hannu wajen ci gaba da taimaka wa al’umma,” in ji Barkindo.

Ya ce a ranar Lahadin da aka fara taron na kwana shida, akwai tsofaffin gwamnoni da suka halarta kuma suka yi jawabi kan irin yanayin da suka shiga bayan barin mulki.

“Akwai gwamnan da ya bayyana a wajen cewa bayan ya bar mulki kusan daina kiransa aka yi a waya, sai a shafe lokaci babu wanda ya kira shi.

“Akwai kuma wanda da ya je shiga jirgi zai yi wata tafiya a filin jirgin sama, ya manta cewa a lokacin ba shi da ‘yan rakiya da ‘yan kai-kawo da za su tuna masa lokacin tashin jirgi.Haka ya sha’afa har jirgin ya tafi ya bar shi.

“Akwai sauye-sauye da dama da mutane za su gani bayan barin su mulki musamman ta bangaren ni’imomin da mulkin ke zuwa da su,” in ji mai magana da yawun kunfiyar gwamnonin.

An horar da sababbin gwamononin kan yadda za su tafiyar da gwamnati /Hoto: NGF

Ya jaddada cewa don haka dole a nuna wa gwamnoni masu barin gado irin wadannan darussan don su shirya wa abubuwan da za su gani sosai.

“An yi jawabai iri-iri kan yadda barin mulki yake, don ba karamin abu ba ne. Mulki na shagawabar da mutane, don haka akwai bukatar nusar da mutum don ya san cewa to daular fa ta kare,” ya ce.

Su waye mahalarta taron?

Abdulrazaque Barkindo ya ce an gayyato masu gabatar da jawabai daga fadin duniya da suka hada da shugabannin gwamnatoci da jami’an diflomasiyya da manyan ‘yan kasuwa.

Kazakila akwai sauran masu ruwa-da-tsaki da suka taba cimma nasarori a tarihin gwagwarmayarsu wadanda za su karfafa gwiwar sababbin gwamnonin wajen zage dantse da yin abin da ya dace.

A cikin bakin har da wasu tsofaffin gwamnonin jihojin Virginia da Maryland na Amurka, Terry McAuliffe da O’Malley Martin Joseph. Sannan akwai Magajin Garin Birnin NewYork na Amurka Eric Adams, wanda ya halarci taron ta bidiyo ta intanet.

Shi O’Malley ya yi fice sosai wajen rage aikata munanan ayyuka lokacin da yake gwamnan Jihar Maryland yayin da shi kuma McAuliffe ya yi zarra wajen inganta tsarin kiwon lafiya da ilimi a jihar Virginia.

Barkindo ya ce shi kuwa Magajin Garin New York an gayyace shi saboda girman tattalin arzikin birnin da yake jagoranta da shahararsa a duniya.

Cikin mahalarta taron har da shugabannin manyan hukumomin duniya/ Hoto: NGF

“Kuma mun gayyaci Farfesa Peter Anyang Nyongo, gwamnan Lardin Kisumu na kasar Kenya, wanda ya kware wajen inganta rayuwar mutane a fannin kiwon lafiya tare da rage mugun talaucin da ya addabi yankin.

Akwai kuma tsofaffin gwamnonin Nijeriya da shugabannin manyan hukumomin duniya ‘yan kasar irin su Dr Ngozi Okonjo Iweala, Daraktar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da Amina Mohammed, mataimakiyar Sakatare Janar ta MDD da kuma Dr Akinwumi Adeshina, Shugaban Bankin Cigaban Kasashen Afirka.

Matan sababbin gwamnoni

Masu magana kan ce ba za a yi tuya a manta da albasa ba.

Watakila ganin irin rawar da matan gwamnoni kan taka a mulki da irin yadda suke fito da nasu tsare-tsaren ya sa Kungiyar NGF ba ta bar zu a baya ba wajen yi musu nasu horon.

Kungiyar gwamnonin kasar ta ware ranakun karshe na taron wato Alhamis da Juma’a 18 da 19 ga watan Mayu don wayar da kan matan gwamnoni masu jiran gado kan tafiyar da tsare-tsarensu.

“Za a yi wa matan sababbin gwamnoni 18 da za su kasance a cikin kungiyar matan gwamnoni ta kasa fadakarwa kan abin da ya kamata su yi wa mata da irin ci gaban da ya kamata su samar musu,” kamar yadda Barkindo ya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here