Najeriya ta kammala kwashe ɗalibanta da ke Sudan

0
104

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da kammala aikin kwashe ɗalibai ‘yan ƙasar da ke karatu a ƙasar Sudan Waɗanda ɓarkewar rikici tsakanin sojojin gwamnati da na RSF ya rutsa da su.

Ma’aikatar jin kai da kare afkuwar bala’i ta Najeriya da ta yi aikin kwashe daliban da haɗin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta NEMA, da ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen Sudan da Masar ne suka sanar da hakan.

Babban sakatare a ma’aikatar jin kai da kare afkuwar bala’i a Najeriya Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya shaida wa BBC cewa sai da aka bi matakan da suka dace domin tabbatar da kariyar ɗaliban, kafin a fara kwashe su.

Ya ce jirgin da ya sauka a ranar Asabar shi ne jirgi na 15 kuma shi ne na ƙarshe da ya ƙwaso ɗaliban Najeriyar da ke karatu a Sudan.

”Jirage huɗu na farko da suka kwaso ɗailbai kusan 800, sun taso ne daga ‘Aswan’ na ƙasar Masar, sai kuma ragowar 14 da suka taso daga Port Sudan”, in ji shi.

Dakta Gwarzo ya ce sun kwaso duka wani ɗan Najeriya da ke Sudan wanda ya nemi taimakonsu, kuma ya kasance yana da takardu.

Ya ce kashi 95 cikin 100 na mutanen da suka kwaso Dalibai ne da ke karatu a ƙasar ta Sudan.kashi 95 cikin 100 na mutanen da suka kwaso Dalibai ne da ke karatu a ƙasar ta Sudan.

Dakta gwarzo ya ce ”matsalar da muka samu da masu motocin bas-bas ce ta haddasa tsaikon da aka samu wajen ƙwashe ɗaliban a kan lokaci”.

Amma duk da haka a cewarsa babu ƙasar da ta iya kwaso adadin mutanen da suka kai na Najeriya a cikin wannan lokacin.

Game da matsayin karatun ɗaliban kuma dakta gwarzo ya ce sun tattauna da ma’aikatar ilimi ta ƙasar, wadda ya ce ta aiko musu da wani jadawali da za su rubuta sunayen ɗaliban, domin duba yiwuwar yadda za a tallafa wa ɗaliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here