Dakatar da shigo da manja: Kwararru a Najeriya sun bukaci a zuba jari mai yawa a fannin

0
108

Kwararru a fannin noman Kwakwar Manja sun yi kira da a zuba jari a nomanta, mussaman don a kara bunkasa nomanta a kasar nan.

A wata hira da ban da ban da aka yi da su a jihar Legas, kwararrun sun mayar da martani ne kan rahoton da aka wallafa a kwanan baya cewa, Nijeriya ta shigo da Manja da kudinsa ya kai Naira biliyan 299.6 daga 2017 zuwa 2022.

Rahoton na tsakiyar shekara wanda hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta wallafa ya nuna cewa, Danyen Manjan na daga cikin manyan kaya biyar da ake shigo wa da su cikin Nijeriya.

Daya daga cikin kwararru Farfesa  Adetunji Iyiola ya koka kan yadda ake shigo da Manjan cikin kasar nan,duk da cewa Nijeriya ta kasance kasar noma.

A cewar Iyiola, akwai bukatar a habaka noman Kwakwar Manja a kasar nan, musamman ta hanyar yin amfani da dabarun zamani ma yin noma.

Ya bayyana cewa,ganin cewa fannin ana samun dimbin kudaden shiga, akwai bukatar a zuba jari mai yawa a fannin a kasar nan tare da kuma zuba jari wajen sarrafa shi.

“Muna da mutane masu kunbar susu da dama a kasar nan a saboda haka akwai bukatar su zuba jarinsu a fannin wajen nomanta da kuma sarrafa ta yadda za ta kai har ana fitar da ita zuwa ketare.

A cewarsa, a zaman mu na kasar, bai kamata ace muna shigo da Manja ba domin Allah ya wadace mu da kasar yin noma mai kyau, musamman a jihohin Osun da Ondo.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta zuba jari a fannin, mussaman wajen kara fadada noma noman ma Kwakwar Manja a kasar nan , inda ya kara da cewa, akwai kuma bukatar a samar wa da manoman na Kwakwar Manja kayan nomanta na zamani don a kara samar da ita fa yawa a kasar nan.

A cewarsa, akwai kuma bukatar gwamnatin ta kara taimaka wa masu sarrafa ta a cikin kasar, inda hakan zai sa a rage shigo da ita daga kasar waje, mussaman don a kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Shi ma a na sa bangaren daya kwararen a fannin Mista Akin Alabi yk bayyana cewa, dole ne a kara yin kokari wajen sarrafa ta a cikin kasar nan, mussaman don a rage shigo da ita daga kasar waje.

Ya bayyana cewa, akwai kuma bukatar a samar wa da manoman ta ingantacce Iri don su samu riba mai yawa bayan sun yi girbi.

Ya sanar da cewa, muna da bukatar samun masu noman Kwakwar Manja a kasar nan domin muna da kasar yin noma mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here