Tasirin kuɗi a zaben shugabannin majalisun Najeriya

0
117

Wasu kuma na ganin tasirin kuɗi na cikin manyan matsalolin da ke janyo nakasu ga tsarin dimokraɗiyya ciki har da batun tafiyar da majalisa a Najeriya.

Wani tsohon ɗan majalisar jiha a Kano, Hon Rabi’u Saleh Gwarzo ya ce rashin ‘yancin cin gashin kai musamman a matakin jiha na da alaƙa da zama ‘yan amshin-shata a ƙasar.

A cewarsa duk lokacin da aka ce wani abu ya samu majalisa, amma sai ta ɗauki ƙoƙo ta tafi ga gwamnati don neman kuɗin kamar sayen ababen hawa da shirya tarukan ƙarawa juna sani, wannan ba ƙaramar matsala ba ce.

Ya ce irin wannan yanayi na ɗaukar ƙoƙo don samun biyan buƙatun wasu haƙƙoƙi daga gwamnati, yana ba da yanayi da gwamnatin ke zuwa da wasu abubuwa da take so a yi mata, ko da ana ganin ba sa kan doka.

Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce dole ne sai majalisa ta yi nazari da kanta kan harkokin kuɗi tsakaninta da ɓangaren zartarwa.

“Sai ta tsarkake kanta wajen mu’amalarta da ɓangaren zartarwa ta fuskar hada-hadar kuɗi. Mu’amalarta ta cikin gida game da kuɗi, a fassara kowanne kuɗi da ya shigo, a fayyace abin da aka ce a yi da shi, da kuma yadda za a yi da shi”.

Ya ce dukkan wanda zai yi gyara, sai ya fara duban kansa ya yi gyara.

A cewarsa, kamata ya yi ‘yan ƙasar su mayar da hankali wajen sa ido kan majalisun ƙasar don ganin kuɗaɗen da ake ware musu, ana amfani da su wajen inganta tsarin ayyukan majalisa da kuma bibiyar harkokin ɓangaren zartarwa.

Kabiru Sufi ya ce aikin majalisa, harka ce mai buƙatar kashe ɗumbin kuɗaɗe, hatta aikinsu na bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa.

Ya ce kuma duk lokacin da aka samu canji, aka zaɓi sabbin ‘yan majalisa akwai buƙatar a horas da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here