Rikicin Hausawa da Amotekun: Gwamnati ta yi mana adalci – Sarkin Hausawa

0
104

Sarkin Hausawan Ado-Ekiti a Jihar Ekiti, Alhaji Abdullahi Yusuf ya nuna damuwa da bakin cikin yadda wasu jama’arsa ‘yan kasuwa suka bijire wa umarnin mahukumta a kan batun komawarsu sabuwar kasuwar Olope da ya haifar da rikici a tsakaninsu da jami’an tsaro na Amotekun da ya yi sanadin mutuwar mutum daya.

A hirarsa da Aminiya, Sarkin Hausawan ya ce “A gaskiya tsakani da Allah Gwamnatin Jihar Ekiti ta yi mana adalci a kan wannan batu domin an ba mu wa’adi na isasshen lokaci tare da yawaita yin shela da yekuwa cikin harshen Hausa domin amfanin mutanena a game da muhimmancin komawa sabuwar kasuwa ta Olope da illar ci gaba da zama a tsohuwar kasuwar Atikankan da ta cunkushe.

“Tun cikin watan azumi mahukumta suka so mu tattara kayanmu daga tsohuwar kasuwar zuwa sabuwa, amma ni da kaina na nemi alfarmar a kyale mu zuwa bayan sallah.

“Bayan gwamnati ta amince da bukatar da muka nema zuwa wannan lokaci da mafi yawa daga cikin jama’ata muka koma sabuwar kasuwa, sai wasu ‘yan kalilan daga ciki ne suka bijire wa umarnin mahukumta, wanda shi ne dalilin turo jami’an tsaro na Amotekun domin tilasta tashin su daga tsohuwar kasuwar zuwa sabuwa.”

Wata majiya da aka sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa “A shekaranjiya Alhamis ne lamarin ya so ya kazanta a lokacin da jami’an Amotekun suka umarci ‘yan kasuwan su tashi su koma sabuwar kasuwa da suka ki bin wannan umarni, a maimakon haka ma sai suka rinka jifan jami’an da duwatsu da ya haifar da barkewar rikici a tsakaninsu da ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasuwa hudu.”

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin ’yan sanda na Jihar Ekiti, Sunday Abutu ya ce bayan samun labarin aukuwar lamarin rundunar ta hanzarta aikawa da jami’anta da suka kwantar da rikicin kafin ya kazanta.

Ya tabbatar da cewa jami’an Amotekun biyu sun samu raunuka da yanzu suke kwance a asibiti.

Ya ce an kama mutane hudu da ake zargi da haddasa rikicin kuma kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Dare Ogundare ya bayar da umarnin bincike domin gano ainihin dalilin aukuwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here