NiMet ta yi gargadi kan saukar mamakon ruwan sama da tsawa a arewacin Najeriya

0
103

Hukumar da ke sanya ido kan yanayi a Nijeriya, NiMet, ta yi gargadi game da saukar mamakon ruwan sama da tsawa a wasu jihohin arewacin Nijeriya a kwanakin da ke tafe.

Ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Alhamis.

Bayanan sun nuna cewa jihohin Borno da Taraba da Gombe da Bauchi da kuma Kano za su fuskanci saukar mamakon ruwan sama mai tafe da tsawa.

An yi hasashen ruwan saman zai yadu zuwa wasu yankuna da ke kudancin kasar, kazalika sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran tsawar za ta bazu zuwa wasu wurare ciki har da wasu garuruwa a jihar Filato.

NiMET ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar yankunan su fuskanci rushewar gine-gine da karyewar bishiyoyi da falwayoyin wutar lantarki da sauransu.

Don haka ta shawarci jama’a su kasance masu kula da zama a gida a lokutan da ake ruwan sama mai karfi gaske da ka iya zuwa da walkiya.

Sanarwa ta kuma bukaci Ma’aikatar Sufurin jiragen sama a kasar ta tabbatar tana amfanar da kanta da rahotannin yanayi da Hukumar NiMET ke fitarwa a-kai-a-kai.

Har wa yau, sanarwar ta ce ruwan saman zai iya haifar da ambaliya, don haka ta shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan.

NiMET ta kuma bukaci hukumomi da ke da alhakin kula da kuma takaita aukuwar bala’i da daidaikun mutane su tashi tsaye don dakile asarar rayuka da dukiyoyi da ake samu a lokutan damuna a Nijeriyai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here