NYSC: ‘Yan Najeriya suna murnar shekara 50 da fara shirin yi wa kasa hidima

0
109

Mutane a shafukan sada zumunta a Najeriya suna ta murnar bikin cika shekara 50 da fara hidimar kasa, wato NYSC.

An kaddamar da shirin ne ranar 22 ga watan Mayu na shekarar 1973. Wato sai ranar 22 ga watan Mayun nan ne zai cika shekara 50.

Sai dai da yake batu ne na abu-namu-maganin-a kwabe-mu, tuni matasa har ma da manya da suka taba yin hidimar, suka fara tattaunawa kan batun a zaurukan sadarwa na zamani.

A bin lamarin da TRT Afrika ta yi sosai, ta gano dumbin mutanen da suka yi bautar kasa a baya suna yada hotunansu a lokacin da suke aikin hidimar kasa.

A shafin Twitter dai, maudu’in #NYSCat50 na daga cikin wadanda suka fi tashe inda aka yi amfani da shi sau fiye da 20,000 a ranar Laraba.

A Facebook ma dai ba ta sauya zani ba, don kuwa fiye da mutum 167,000 ne suka dinga magana a kan batun.

A Instagram da Tiktok ma duk zancen daya ne, murnar cikar shirin hidimar kasa shekara 50 da farawa.

Mutane sun yi ta bayyana yadda suke kewar zamanin hidimar kasa, tare da wallafa hotunansu sanye da koren kaki da riga da hula da takalman da ake gane ‘yan hidimar kasar da su.

Ga dai wasu daga cikin sakonnin da mutane suka yi ta wallafawa:

Ibrahim Umar ya wallafa wani gajeren sako da ke nuna godiyarsa ga Allah a kan samun damar yin hidimar: “NYSC a shekara 50 “me kuke karyata wa daga cikin ni’imomin Ubangijinku”.

Shi kuwa Jubril A Gawat ya lissafo wasu jerin abubuwa da suka faru ne a lokacin da yake zaman mako uku na sansanin hidimar kasar.

Sai dai a yayin da mafi yawan mutane bege suke da tunawo da dadin shirin a zamanin da suka yi shi, irin su Abdulaziz T Bako cewa ya yi ba ma ya son tuna lokacin.

Abdulaziz, wanda likita ne mazaunin kasar Amurka kuma fitaccen mai amfani da Facebook, bai bayyana dalilin hakan ba a gajeren sakon da ya wallafa a shafinsa.

Da ma manufar shirin na NYSC, wanda gwamnatin mulkin soja ta Nijeriya ta Janar Yakubu Gowon ta kirkiro, shi ne kawo hadin kan ‘yan kasa, bayan yakin basasa a kasar.

Matasa da suka kammala karatun digiri ko babbar difloma ta HND su ne suke shiga shirin, inda a kan tura su jihohi daban-daban na Nijeriya don aiki a ofisoshi da al’ummomin yankin.

Matasa kan samu horo daga sojoji, da kuma koyon sana’o’i da za musu amfani a rayuwarsu.

Sai dai ga duk wanda ya wuce shekara 30, to ba ya yin hidimar kasar.

Sannan gwamnati kan ba da wani dan alawus da ke taimakon matasan, kazalika wuraren da aka tura su yin aiki kamar hukumomi da ma’aikatuma kan ba su wani abu.

A kan shafe mako uku a sansanin hidimar kasa kafin daga bisani a aika da mutum wajen da zai shafe shekara yana koyon sanin makamar aiki.

Yawanci kuma a kan dauke mutum daga jiharsa ta haihuwa ko inda ya yi karatu ne a cilla shi wani yankin daban, amma a kan bar masu wani babban uzuri na rashin lafiya, ko matan aure a bar su a inda mazajensu suke zama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here