Man Utd za ta sayi Ramos, Chelsea na son riƙe Felix

0
105

Manchester United ta tattauna da Benfica domin sayen matashin dan gabanta na Portugal Goncalo Ramos mai shekara 21 a kan farashin da ya kai fam miliyan 100 hadi da wasu tsarabe-tsarabe. (Mirror)

Chelsea na fatan idan har ta yi nasarar nada Mauricio Pochettino a matsayin sabon kociyanta hakan zai iya sa ta shawo kan N’Golo Kante, ya yarda ya kulla sabon kwantiragi a Stamford Bridge din. (Telegraph)

Haka kuma Chelsean a shirye take ta bayar da Pierre-Emerick Aubameyang da Marc Cucurella, a cinikin neman rike dan gaban Portugal Joao Felix dindindin wanda Atletico Madrid ta ba ta aronsa . (Standard)

Manchester United za ta yi gogayya da Arsenal da kuma Chelsea wajen sayen Declan Rice bayan da dan wasan na Ingila ya taka rawar gani a wasan da West Ham ta yi da su ranar Lahadi. (Sun)

West Ham na sha’awar dan gaban Coventry City Viktor Gyokeres dan Sweden. (Mirror)

Arsenal na da kwarin gwiwa Bukayo Saka, zai sanya hannu a wani sabon kwantiragi na shekara biyar wanda zai rika karbar albashin da ya kai fan 300,000 kafin karshen kakar nan. (TalkSPORT)

Newcastle na daga cikin kungiyoyin Premier da zasu yi gogayya da Inter Milan da Juventus a kan dan bayan Monza dan Brazil Carlos Augusto. (Calciomercato)

Liverpool ta yi nisa a tattaunawar da take ta neman nada Jorg Schmadtke Bajamushe a matsayin sabon darektanta na wasa. (Mail)

David de Gea ya yarda da sabon kwantiragi da Manchester United, amma kuma an rage masa wasu abubuwa a yarjejeniyar sannan kuma babu tabbas zai ci gaba da zama golan kungiyar na farko. (Telegraph)

Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila James Milner, ya yi watsi da tayin da Everton ta yi masa inda ya zabi tafiya Brighton idan kwantiraginsa da Liverpool ya kare da bazara. (Football Insider)

Tsohon kociyan West Brom da Barnsley Valerien Ismael ya yi nisa a tattaunawar zama sabon mai horad da Watford. (Athletic)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here