An fara kalubalantar Bola Tinubu a Najeriya

0
105
Yayin da ake shirye-shiryen kaddamar da zababbun shugabanni a Najeriya, kotunan sauraron kararrakin zabe sun fara sauraron bukatun soke zabe da aka shigar a gabansu.

Da ranar Litinin din nan ne kotu a Abuja babban birnin Najeriya, ta fara sauraron kararrakin da ke kalubalntar nasarar zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, wanda hukumar zaben Najeriyar ta ce shi ne ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da aka yi.

‘Yan sanda a Abujar sun datse hanyoyi saboda takaita zirga-zirga a lokacin da ake sauraron karar da babban mai adawa da Tinubu; Atiku Abubakar na jami’yyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour suka shigar.

A wajen harabar kotun an ga wasu kimanin mutum 100 na zanga-zanga cikin lumana, inda suke bukatar da kada a rantsar da Bola Tinubun na jam’iyyar APC.

Manyan masu adawar dai na kalubalantar hukumar zabe ne da taka dokokinta da kanta gami shirya magudin da suka kai ta ga bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Zaben na watan Fabarairu dai ya kasance mafi karancin fitowar masu zabe da aka gani a Najeriya, tun bayan dawo da mulkin dimukuradiyya a cikinta a shekarar 1999.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here