Ƙasashen ƙetare ne ke rura wutar rikici a Afirka – Bazoum

0
97

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Bazoum Mohamed ya yi zargin cewa ƙasashen waje ne ke rura wutar rikice-rikicen da ke faruwa a Afirka.

A wata hira da ya yi da BBC, shugaba Bazoum ya ce ƙasashen ƙetare ne ke ƙara ta’azzara rikicin ta hanyar mara wa duka ɓangarorin da ke rikici da juna a yaƙe-yaƙen da ake yi a nahiyar.

”In ka ga ana yaƙi a ƙasar Afirka to akwai ƙasashen ƙetare da ke mara wa ɓangarorin da ke yaƙi da junan baya”.

Shugaban ya ce kuma irin waɗannan ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU ba ta da ta cewa a kansu.

Dan haka kar a yi tsammanin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ta AU za ta iya yin wani abu kan abin da ke faruwa a Sudan”.

Ya yi gargaɗin cewar rikicin da ake yi a ƙasar Sudan yana da matuƙar illa ga ƙasashen Afirka, saboda a cewarsa yaƙin zai iya shafar ƙasashen.

‘Yaƙin Sudan zai shafi ƙasashen Afirka’

Bazoum ya ce duk da ƙoƙarin da ƙasashen duniya ke yi na shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin, dole sai ƙasashen Afirka sun yi wa kansu gata, ta hanyar yaƙi da yaɗuwar makamai.

Shugaban na Nijar ya ce shugabannin Afirka na baƙin cikin abin da ke faruwa a ƙasar Sudan ɗin, saboda a cewarsa irin wannna yaƙin basasa yakan ɗauki shekaru kafin a kawo ƙarshensa.

Ya ce a baya ƙasarsa – wadda ta yi makwaftaka da ƙasashen Mali da Libya – ta fuskanci irin matsalolin sakamakon tashe-tashen hankulan da aka samu a ƙasashen Malin da Libya.

”Bayan fiye da shekara 10 da faruwar rikice-rikice a ƙasashen biyu har yanzu ba a kai ga warware matsalolin da suka faru ba”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk matsalolin da ake fuskanta a yanzu a yankin ƙasashen Sahel ya faro ne sakamakon tashe-tashen hankulan da suka faru a ƙasashen Libiya da Mali.

”Hakan ya faru ne sakamakon irin miyagun makaman da suka yaɗu a wannan yanki namu duk a sanadin yaƙin da aka samu a ƙasashen biyu” a cewar Bazoum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here