Trump zai biya matar da yai lalata da ita diyyar $5m

0
103

Masu taya alƙali hukunci sun nemi tsohon shugaban na Amurka ya biya diyyar jimillar kuɗi har dala miliyan biyar ga E Jean Carroll saboda yin amfani da ƙarfi da kuma ɓata mata suna.

Wannan ne karon farko a tarihi, da aka taɓa samun wani shugaban Amurka da auka wa mace da lalata.

Kafin a karanto hukuncin kotun, E Jean Carroll ta zauna shiru, cikin tsakiyar lauyoyi.

Ta riƙe hannuwan lauyoyinta, lokacin da ake karanto hukuncin, inda ta zura idanu gaba, tana kuma ɗan sunkuyar da kai lokacin da masu taya alƙali hukunci suka ba da sanarwar cewa sun samu tsohon shugaban na Amurka da laifin ɓata mata suna.

Ta yi tattausan murmushi a lokacin da suka ce gaba ɗayansu sun yarda, sai Trump ya biya ta diyyar dala miliyan biyar.

Bayan masu taya alƙalin hukuncin sun tashi sun bar kotun ne kuma, sai lauyan Trump, Joe Tacopina ya miƙe, ya je wurin Carroll inda ya yi musabaha da ita.

“Ina taya ki murna,” ya ce mata. “Allah taimaka, shi kenan?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here