Home Labarai Wasanni Kungiyar Saudiya ta bai wa Messi Fam miliyan 260 don ya buga...

Kungiyar Saudiya ta bai wa Messi Fam miliyan 260 don ya buga mata kwallo

0
117

Akwai yiwuwar Messi ya ci gaba da zama a PSG har zuwa karshen wannan kaka kafin ya yanke shawara game da makomarsa.

Kimanin wata guda kenan da aka yi wa Messi wannan gwaggwabar tayin amma bai yi gaggawar amincewa da ita ba.

A maimakon haka, dan wasan na Argentina ya ci gaba da mayar da hankalinsa kan wasannin PSG a wannan kaka duk kuwa da dakatarwar da kungiyar ta yi masa ta tsawon makwanni biyu.

Dan wasan na fatan kammala wannan kaka da kofin gasar Lig ta Faransa a hannunsa

Wasu rahotanni a Spain sun ce, dan wasan mai shekaru 35 zai raba gari da PSG a karshen wannan kaka kuma ana sa ran zai ki amince wa komawa Barcelona tare da tafiya zuwa yankin gabas ta tsakiya.

Babu mamaki Messi din zai bi sahun tsohon abokin hamayyarsa a duniyar tamola, Cristiano Ronaldo wanda ya koma Saudiya da taka leda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here