Ba ma shirin daukar fansa a kan Real Madrid – Guardiola

0
126

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce za su yi “gagarumin kuskure” idan suka nemi “daukar fansa” a kan Real Madrid a wasan kusa da karshe da za su fafata na Gasar Zakarun Turai.

Ya bayyana haka ne yayin da yake hira da manema labarai gabanin karawar da za su yi ranar Talata a Santiago Bernabéu.

A bara, City na gaban Madrid da 5-3 a minti na casa’in a zagaye na biyu na wasan kusa da karshe, amma ‘yan madara suka zage dantse suka fitar da City.

Don haka ne yanzu Guardiola ya bukaci yaransa su yi bakin kokarinsu wajen lashe Kofin na Zakarun Turai.

“Ba mu zo nan domin daukar fansa ba, mun zo ne domin mu samu dama,” in ji Guardiola.

“Duk abin da ya faru, ya faru ne a baya. Zai kasance gagarumin kuskure mu rika tuna shi.

Kocin City ya ce babban darasin da suka koya game da abin da ya faru a bara shi ne su zage dantse su yi wasan da ya dace domin samun sakamako mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here