Barcelona na son Gundogan, Napoli za ta rike Osimhen

0
122

Barcelona na da kwarin gwiwar kammala cinikin dan wasan tsakiya na Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan. (90min)

Aston Villa kuwa na shirin sayen dan gaban Serbia Dusan Vlahovic, daga Juventus. (Football Insider)

Tottenham ta bukaci Barcelona da ta fadi farashin da ta yi wa dan wasanta na tsakiya Franck Kessie, dan Ivory Coast. (Sport )

Bayanai na nuna cewa Liverpool ba ta tuntubi Brighton ba a kan maganar sayen dan wasan tsakiya nata Alexis Mac Allister, dan Argentina. (Athletic)

Shugaban Napoli Aurelio de Laurentiis ya ce zakarun na gasar Italiya ta Serie A ba za su sayar da dan wasansu na Najeriya Victor Osimhen, ba, wanda manyan kungiyoyi da dama na Turai ke son saye a bazara. (Cinque Minuti, daga Mail)

Tsohon kyaftin din Gabon Pierre-Emerick Aubameyang zai bar Chelsea – kuma yana son komawa Barcelona. (Fabrizio Romano)

A shirye Aston Villa take ta biya kudin da Fulham ta sa fam miliyan 60 a kan dan wasanta na tsakiya dan Portugal Joao Palhinha. (Football Insider)

Wakilin dan wasan tawagar Portugal Joao Cancelo ya gana da Barcelona kan sayen dan bayan na Manchester City wanda ke zaman aro na shekara daya a Bayern Munich, tare da zabin sayensa. (Sport )

Manchester City za ta duba yuwuwar zawarcinmatashin dan wasan tsakiya na Bayern Munich Ryan Gravenberch, na Holland wanda ake dangantawa da Liverpool, idan har kungiyar ba ta samu nasarar sayen Jude Bellingham, na Ingila ba daga Borussia Dortmund. (Mirror)

Eden Hazard ya kuduri aniyar ci gaba da zama har shekararsa ta karshe ta kwantiraginsa da Real Madrid, duk da yadda ba a sa shi sosai a wasa a kungiyar. (Cadena Cope, daga Marca)

Roma ta cimma yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Faransa Houssem Aouar inda zai koma kungiyar ta Italiya a bazara lokacin da kwantiraginsa zai kare a Lyon. (Sky Sports Italia )

Adam Lallana ya taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan tsohon abokin wasansa James Milner zuwa Brighton daga Liverpool.

Tsohon dan wasan na Ingila na dab da cimma yarjejeniyar komawa Brighton din. (Football Insider)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here