Adadin wadanda ambaliyar ruwa ya kashe a Congo ya kai kusan 400

0
120

Akalla gawarwaki 394 ne aka gano bayan ambaliyar ruwa a makon da ya gabata, a cewar Thomas Bakenga, mai kula da yankin Kalehe inda kauyukan da abin ya shafa suke, bayan a ranar asabar aka sanar da adadin  mutane a kalla 203 da suka mutu.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shatata ranar Alhamis a yankin Kalehe da ke lardin Kivu ta Kudu ya haifar da tunbasar koguna, lamarin da ya janyo zaftarewar kasa da ta mamaye kauyukan Bushushu da Nyamukubi.

Jami’in ya kuma kara da cewa an gano gawarwakin mutane 142 a Bushushu, 132 a Nyamukubi sannan 120 an gano suna shawagi a tafkin Kivu da ke kusa da Idjwi, tsibiri dake tsakiyar babban tafkin aman wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here