An ceto mutum 58 da aka yi garkuwa da su a Abuja

0
111

 

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Abuja babban birnin kasar ta ce ta ceto mutum 58 da aka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan birnin SP Josephine Adeh ta fitar, ta bayyana cewa an ceto mutanen ne daga dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu ta Jihar Kogi, wanda ke da iyaka da Dajin Sardauna na Jihar Nasarawa.

Haka kuma ta ce akwai wasu da aka ceto daga wasu sansanonin ‘yan garkuwa da mutanen da aka gano a wasu wurare a Abuja.

“A lokacin da barayin suka ga jami’an tsaro karkashin jagorancin ‘yan sanda, sai suka soma harbinsu wanda hakan ya ja aka yi musayar wuta.

“An fi karfin ‘yan bindigar inda suka tsere da raunukan harsasai a jikinsu tare da barin wadanda suka kama,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa a lokacin aikin ceton, daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su mai suna Tama Jonathan ya rasu sakamakon raunukan da ya samu inda ya mutu a wurin nan take.

“An kai wa iyalinsa gawarsa domin a binne shi, sauran mutum 58 ana duba su a asibiti kuma za a hada su da iyalansu,” in ji sanarwar.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa ta gudanar da wannan aikin ceton ne tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da ‘yan bijilanti, duk a yunkurin kawo karshen garkuwa da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here