Abin da ya sa wasu manoma a jihar Kano suka ba da hayar gonakinsu

0
106

A yayin da daminar kakar yin noma ta shekarar 2003 ta fara a kasar nan, biyo bayan ci gaba da samun hauhawan farashin takin zamani wasu manoma a jihar Kano sun bayar da hayar gonakansu da wadanda za su iya noma su.

Hauhawan farashin na takin zamani a daukacin fadin kasar nan, na ci gaba da ciwo manoman Tuwo a Kwarya.

Saboda ci gaba hauhawan farashin manoman na ganin ba za su iya mayar da kudaden da suka kashe wajen yin noman ba, ballabta na har su samu wata ribar kirki bayan sun yi noman.

Lamarin na hauhawan farashin har ya fi yin kamari ga kananan manoman, inda wasu daga cikin manoman ma, suka gwammace su daina yin noman ko kuma su rage yin noma a gonakansu a kakar noman ta bana kamar yadda suka saba yi a baya.

Wasu manoma sun ce, farashin takin zamani samfarin NPK 20-10-10 akasari ana sayar da shi daga Naira 15,000 zuwa Naira 17,000.
Sun kara da cewa, ana kuma sayar da takin zamani samfarin Urea daga Naira 21,000 zuwa Naira 22,000.

A cewarasu, ana kuma sayar da takin zamani samfarin Golden NPK kan Naira 25,000.
Sun bayyana cewa, idan aka yi lissafi karamin manomi da ke da a kadada daya ta Shinkafa za ta ci buhunhunan takin zamani akalla takwas, inda jimmlar kudin zai kai Naira156,000.

Bisa ga kididdigar da Cibiyar bunkasa takin zamani ta kasa da kasa ya fitar IFDC ta nuna cewa, Nijeriya ta shigo da takin zamani da ya kai metric tan 706,922 a shekarar 2021, inda kuma aka shigo da wasu sanadaran hada takin zamanin 429,303 a shekarar 2020.

“Idan aka yi lissafi karamin manomi da ke da a kadada daya ta Shinkafa za ta ci buhunhunan takin zamani akalla takwas, inda jimmlar kudin zai kai Naira156,000.”
Bugu da kari, a farkon mulkin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnatin ta kulla yarjejeniya da wasu kamfanonin kasar nan da ke sarrafa takin zamani domin su shigo da kayan da ake hada takin daga kasashen Morocco, Rasha da Ukraine domin a sayar wa manoman a farashi mai sauki.

A yayin da gwamnatin Buhari ta fara yin amfani da wannan tsarin ta hanyar shirin takin zamani ma fadar shugaban kasa (PFI), hakan ya taimaka wajen rage farashin na takin zamani, inda kuma hakan, ya taimaka wa manoman kasar nan matuka.

Dakta Farouk Hamzat, wani mai kamfanin sarrafa takin zamani a jihar Kano ya bayyana cewa, hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na dakatar da shirin na PTI ne ya janyo ci gaba da hauhawan farashin takin zamanin, indabya yi nuni da cewa, farashin zai ci gaba tashi idan har gwamnatin tarayya ba shiga tsakani ba.

“Hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na dakatar da shirin na PTI ne ya janyo ci gaba da hauhawan farashin takin zamanin, indabya yi nuni da cewa, farashin zai ci gaba tashi idan har gwamnatin tarayya ba shiga tsakani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here