Madrid za ta tsawaita zaman Modric, Arsenal na son ɗauko Josip Sutalo

0
127

West Ham za ta buƙaci fan miliyan 100 ga duk mai son sayen ɗan wasan tsakiya na Birtaniya Declan Rice, mai shekara 24. (ESPN).

Chelsea na tunanin ɗauko ɗan wasan gaba na Inter Milan, Lautaro Martinez mai shekara 25. Haka nan Manchester United ma na sanya ido kan ɗan wasan, ɗan asalin ƙasar Argentina. (Footbal Insider).

Chelsea na son ganin mai tsaron raga na Inter Milan ɗan asalin ƙasar Kamaru, Andre Onana mai shekara 27 ya zama babban golanta a kakar wasanni mai zuwa, kuma tana da yaƙinin cewa za ta samu nasarar ɗauko Mauricio Pochettino a matsayin sabon mai horas da ƴan wasa. (Telegraph)

Tsohon mai horas da ƴan wasan Bayern Munich, Julian Nagelsmann mai shekara 35 na son aikin kociyan Tottenham, bayan ya tattauna da hukumomin ƙungiyar mai buga wasan

firimiya ta Ingila (Sky Germany)

Ɗan asalin ƙasar Ingila mai wasa a Borussia Dortmund, Jude Bellingham mai shekara 19 zai sanya hannu kan kwantaragi ta sheka shida da ƙungiyar Real Madrid a kakar bana, wanda hakan zai sanya shi ya zama ɗan wasa na biyu da ya fi samun albashi a ƙungiyar, bayan ɗan wasan gaba Eden Harzard. (Ser Deportivos)

Manchester United ba ta da niyyar ɗaukan Wout Weghorst a matsayin ɗan wasa na dindindin. Ɗan wasan mai shekara 30 ɗan asalin Netherlands ya je United daga Burnley ne a matsayin aro a watan Janairu.

Ɗan wasan tsakiya na Croatia, Luka Modric mai shekara 37 na shirin tsawaita kwantaraginsa a Real Madrid har nan da 2024. (Relevo)

Manchester City na ci gaba da yunƙurin ganin ta ɗauki mai mai tsaron raga na Ingila Spike Brits mai wanda ke wasa a matakin ƴan ƙasa da shekara 16, daga ƙungiyar AFC Wimbledon. (Fabrizio Romano)

Arsenal na sanya ido kan ɗan wasan tsakiya ɗan asalin Croatia mai wasa a Dinamo Zagreb, Josip Sutalo. (Evening Standard).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here