‘Yan wasa 10 na duniya da suka fi samun kudi a 2023

0
126

Shafin mujallar Forbes ya wallafa rahoton jerin ‘yan wasan motsa jiki su goma, da suka fi kowa samun kudi a fagensu cikin shekara guda.

Sun samu kudi a jumlace, kimanin dala biliyan 1.11 idan ba a cire haraji da kudin dillalai ba. Wannan adadi ya nuna karin kashi 12% daga adadin bara na dala miliyan 990.

Wannan shi ne mafi girman adadi da aka taba samu a tarihi tun shekarar 2018. Ko a 2018 din ma, da ma tarin kudin da dan wasan kokawa Floyd Mayweather Jr ya samu ne, wanda ya kai dala miliyan 285.

Na 1: Cristiano Ronaldo (dala miliyan 136)

Ronaldo ne ke kan gaba inda ya samu tsabar kudi da ya kai kimanin dala miliyan $136, wanda ya kunshi dala miliyan 46 na albashin buga wasa, da kuma karin dala miliyan $90 daga shiga talla da sauran ayyuka ga kamfanoni.

Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal ne mai shekaru 38 da haihuwa. Shi ya fi kowa a duniya tarin masoya a shafukan sada zumunta da suka kai miliyan 850, a Facebook, da Instagram da Twitter.

Bayan rashin samun tagomashi a zaman shekara daya da rabi da ya yi a Manchester United, Cristiano Ronaldo ya tsallake zuwa Saudiyya inda ya shiga kungiyar Al Nassr.

A kwantiragin da ya rattaba hannu kai a watan Janairu, ya samu albashi ninkin na baya, wanda ya kai kimanin dala miliyan 75.

Na 2: Lionel Messi (dala miliyan 130)

Lionel Messi dan kasar Argentina yana da shekaru 35 a duniya. A halin yanzu Messi na taka leda a kungiyar Paris Saint Germaine da ke birnin Paris na Faransa.

Amma ana ta rade-radin zai koma kungiyarsa ta baya, wato Barcelona da ke Sifaniya.

Akwai wasu rade-radin da ke danganta shi da kungiyoyin kwallo na kasar Saudiyya, inda ake sa ran zai hade da babban sa’ansa, Cristiano Ronaldo mai buga wa Al Nassr wasa.

Ya samu kudin talla daga kamfanonin Adidas, da Budweiser da PepsiCo, da Socios, da sauransu.

Messi ya ciyo wa kasarsa ta Ajantina kofin duniya na kwallon kasa a watan Disambar bara, kuma a watan Oktoba ya kafa kamfanin zuba jari mai suna Play Time.

Na 3: Kylian Mbappé (dala miliyan 120)

Kylian Mbappé, dan kasar Faransa, mai shekara 24 kacal ya zo na uku da kudin da ya kai dala miliyan 120.

A bara Mbappe ya zo na 35 a wannan jeri, sai ga shi a bana ya zo cikin goman farko, kuma shi kadai ne wanda bai kai shekaru 30 ba a cikinsu.

A watan June Mbappe ya zamo ambasadan talla na farko a kamfanin Sorare, wanda kamfanin kirifto ne da yake gudanar da gasar wasanni ta gangan, wato fantas.

Na 4: LeBron James (dala miliyan 119.5)

Dan wasan kwallon kwando, dan asalin Amurka, LeBron yana da shekara 38 a duniya.

Ya samu jumullar kudi dala miliyan 75, inda ya samu dala miliyan 44.5 a falin wasa, da kuma dala miliyan 75 a waje.

Na 5: Canelo Álvarez (dala miliyan 110)

Dan wasan damben boksin dan kasan Meziko, Canelo Álvarez ya samu kudi daga wasanninsa hard ala miliyan $100.

A wajen fili kuma ya samu dala miliyan 10. Yana da shekara 32, Canelo ya samu nasara a gagarumin wasan da ya buga da Dmitry Bivol da kuma Gennadiy Golovkin, cikin watanni da 12 da suka gabata.

A fannin talace-tallace kuwa, Canelo yana aiki da kamfanonin Hennessy da Michelob Ultra, da Yaoca, da manhajar I Can, da kuma kamfanin makamashi Canelo Energy.

Sannan ya shiga kwantiragi da Excel Sports Management a watan Satumba. Haka kuma yana da kamfanin tufafi mai suna da kamfani katin kudi, sannan ya kaddamar da kamfanin barasa na VMC.

Na 6: Dustin Johnson (dala miliyan 107)

Dustin Johnson Ba’amurke ne mai shekaru 38 a duniya. Ya samu dala miliyan 102 a wasannin gwaf da yake bugawa, sai kuma dala miliyan biyar daga talla da kasuwanci.

Johnson shi ne tauraron wasan gwaf na farko da ya yi kaura zuwa gasar LIV Golf, a watan Mayu da ya gabata. Ya kammala gasar a shekarar 2022 da cin kyautar kudi har dala miliyan 35.6.

Barinsa gasar PGA Tour ya janyo masa rabuwa da masu daukar nauyinsa na baya, kamar Royal Bank of Canada.

Amma duk da haka ya samu kudi a bara sakamokon garantin samun tsabar kudi daga lalitar da ta kai dala miliyan 200.

Na 7: Phil Mickelson (dala miliyan 106)

Ba’amurke dan wasan gwaf mai shekara 52, Phil Mickelson ya zo na 31 a jerin bara, lokacin da ya samu dala miliyan 45.3.

A wasannin da ya buga ya samu dala miliyan 104, sannan a wajen fili ya samu dala miliyan biyu.

Forbes ya kiyasata cewa Mickelson ya samu garantin samun dala miliyan daga lalitar dala miliyan 200 don shiga gasar LIV Golf.

A bara ne Phil Mickelson da Dustin Johnson suka bar gasar PGA Tour suka koma gasar da attajiran Saudiya ke daukar nauyi, wato LIV Golf.

Phil daya ne daga cikin wadanda suka samar da kamfanin For Wellness.

Na 8: Stephen Curry (dala miliyan 100.4)

Shahararren dan wasan kwallon kwando, Stephen Curry, ba’amurke ne dan shekara 35. Ya samu kudi daga biuga wasa, har dala miliyan 48.4, sai kuma dala miliyan 52 daga sauran ayyuka.

Albashinsa na dala miliyan 48.1 shi ne mafi girma a gasar NBA ta Amurka a kakar bana.

Ana sa ran zai zaman a farko da zai samu dala miliyan 50 a gasar NBA a kakar 2023-24.

Yana buga wasa a kungiyar Golden State Warriors. A watan Maris ya shiga kwantiragi da Under Armour, wadda za ta ci gaba har bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kwando.

Na 9: Roger Federer (dala miliyan 95.1)

Dan wasan tanis dan asalin kasar Switzerland, Roger Federer, ya samu kusan dala miliyan 95.1, kusan duka a wajen filin wasan.

Yana da shekaru 41 a duniya, kuma abin da ya samu a wasa bai wuce dala dubu dari ba, inda a wajen fili ya samu dala miliyan 95.

Federer ya sanar da yin ritaya daga tani a watan Satumba bayan buga wasan karshe tare da Rafael Nadal a gasar Laver Cup, wadda gasar kasa da kasa ce da ya taimaka wajen samarwa cikin shekarar 2017.

A watan Afrilu, ya sanar da shiga kwantiragin talla da kamfanin RF ta kamfanin tabarau na Oliver Peoples.

Na 10: Kevin Durant (dala miliyan 89.1)

Dan asalin kasar Amurka, Kevin Durant shi ne na goma a wannan jeri na shekarar 2023. Ya samu dala milyan 89.1, inda dala miliyan 44.1 ta zo daga buga wasa. Sai kuma dala miliyan 45 daga sauran kasuwanci.

Kevin mashahurin dan wasan kwallon kwando ne kuma yana da shekaru 34 a duniya. Ya bar kungiyar Brooklyn Nets inda ya koma Phoenix Suns a watan Fabrairu bana.

Wasu daga kamfanonin da yake da alakar kasuwanci suna hada da 35V, da Premier Lacrosse League, da Happy Viking, da League One Volleyball, da Athletes Unlimited, da Major League Pickleball, da kuma Fanatics’ Mitchell & Ness.

Sauran su ne Goldenset Collective, da ScorePlay, da TMRW Sports, sannan yana da kwantiragi da kamfanin nan na Nike, wadda take har tsawon rayuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here