Sama da mutum 100 sun mutu a wata ambaliyar ruwa da ya faru

0
120
Rains-pains-Inside-Nigerias-recurring-flood-menace--1140x570
Rains-pains-Inside-Nigerias-recurring-flood-menace--1140x570

Akalla mutane 109 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a arewaci da yammacin kasar Rwanda, in ji hukumar yada labaran kasar RBA a jiya Laraba, inda ta ambato alkalumma daga hukumomin kasar.

“Ruwan da aka yi a daren jiya ya haifar da iftila’i a lardunan Arewa da na Yamma,” in ji RBA a shafinta na yanar gizo.

“A halin yanzu, alkalumman wucin gadi da hukumomin wadannan lardunan suka wallafa sun ce an sanar da mutuwar mutane 109.”

Mai watsa labaran ya ce har yanzu ruwan na karuwa, wanda ke haifar da barazana ga karin rayuka.

Hukumar ta ce mutane 95 ne suka mutu a Lardin Yamma da ya fi fama da iftila’in da kuma wasu 14 a Lardin Arewa, inda aka ce ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da gidaje da ababen more rayuwa tare da rufe hanyoyi.

Hotunan da aka yada a shafin RBA na Twitter sun nuna cewa gidaje sun lalace, hanyoyin da zaftarewar kasa suka yanke da kuma filayen da ruwan ya mamaye.

“An fara kokarin ba da agaji nan da nan, ciki har da taimaka wa wajen binne wadanda iftila’in ya shafa da kuma samar da kayayyaki ga wadanda gidajensu ya lalace,” in ji ministar da ke kula da ayyukan gaggawa, Marie Solange Kayisire.

Ta yi kira ga mazauna yankin da su kwashe mutane zuwa wuri mafi inganci idan ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A makwabciyar kasar Uganda, mutane shida ne suka mutu a yammacin kasar, sakamakon zaftarewar kasa da afkawar gidajensu, bayan da aka shafe kwanaki ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.

An ce biyar daga cikin wadanda suka mutu ‘yan gida daya ne kuma ‘yan kauye daya ne.

A watan Mayun shekarar 2020, akalla mutane 65 ne suka mutu a kasar Ruwanda sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a gabashin Afirka, yayin da aka samu rahoton mutuwar akalla mutane 194 a Kenya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here