Mata hudu da ‘ya’ya 28, alama ce ta zan iya shugabantar majalisa ta 10 – Doguwa

0
124

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhasan Doguwa, a ranar Laraba, ya ce, dubi ga yadda ya iya rike Mata hudu da ‘ya’yansa 28, wannan alama ce na cewa zai iya shugabantar majalisa ta 10.

Doguwa ya yi wannan furucin ne a martanin da ya mayar kan masu sukarsa da cewa ba shi da kwarewa da hakuri da zai iya maye gurbin shugaban majalisar mai ci a yanzu, Femi Gbajabiamila.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Doguwa ya bayyana cewa masu masa mugun kallo sam basu fahimci halinsa ba.

A halin yanzu dai dan majalisar mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a Kano yana fuskantar shari’a bisa zarginsa da laifin kisan kai, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, barna, da tayar da hankulan jama’a.

Daga shafin: https://www.informationng.com/2023/05/10th-assembly-having-four-wives-28-children-is-proof-ill-succeed-as-speaker-doguwa.html

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here