Buhari zai je London bikin nadin sarkin Ingila

0
123

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bulaguro zuwa kasar Birtaniya domin halartar bikin nadin Sarki Charles III da matarsa Camilla.

Buhari wanda zai samu rakiyar manyan jamiā€™an gwamnatinsa, yana daga ciki shugabannin duniya da Fadar Burkingham ta Birtaniya gayyata domin halartar bikin da zai gudana ranar Asabar, 6 ga watan Mayu.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce gabanin bikin nadin Sarki Charle III, Kungiyar Kasshe Rainon Ingila za ta gudanar da babban taronta a ranar Jumaā€™a 5 ga wata.

Taron, wanda Buhari zai halarta zai tattauna da kan makomar kasashen da muka rawar da matasa za su taka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here