Ronaldo ke kan gaba a cikin ‘yan wasan da ke karbar albashi a duniya

0
151

Shahararrun ‘yan wasan kwallon kafa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da kuma Kylian Mbappe na cikin jerin ‘yan wasa 10 da suka fi amsar albashi a wannan shekarar. 

A cikin jadawalin da jaridar Forbes ta fitar na ‘yan wasa 10 da aka fi biya a wannan shekarar, ya nuna cewar Ronaldo ne ke mataki na daya sai Messi ke biye masa a mataki na biyu ya yin da Mbappe ke a mataki na uku.

Wannan nasarar da Ronaldo ya samu dai ta biyo bayan sauya shekarar da ya yi daga Manchester United a shekarar da ta gabata, inda ya koma Al-Nassr da ke Saudiya, sauyin shekarar da ya sanya shi zama dan wasan da ya fi kowa amsar albashi.

Sauran ‘yan wasan sun hada da dan wasan kwallon kwando LebBron James da shahararren dan wasan damben zamani Canelo Alvarez da ‘yan wasan gora Dustin Johnson da kuma Phil Mickelson da Stephen Curry da gwaron dan wasan Teninnis Roger Federer da kuma Kevin Durant

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here