DA DUMI-DUMI: ‘Yansanda sun cafke dakataccen kwamishinan zaben Adamawa, Ari

0
123

Rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF) ta cafke Barista Hudu Yunusa-Ari, dakataccen kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar Adamawa (REC) domin fuskantar tuhume-tuhume.

A wata sanarwar da ‘yansanda suka fitar a ranar Talata dauke da sanya hannun Kakakin hukumar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce, Yunusa-Ari dai ya shiga hannun tawagar ‘yansanda na sashin tsare-tsare, bibiya da sa-ido kan harkokin zabe ne a ranar Talata a Abuja.

CSP Adejobi ya ce, yanzu haka Hudu yana karkashin kulawar ‘yansanda kuma za su masa tulin tambayoyi dangane da tataburza da kuma dalilan da suka janyo aka gudanar da wasu abubuwan da ba na daidai ba a lokacin kammala zaben gwamnan Jihar Adamawa kwanakin baya.

Ya ce, “Su ma sauran jami’ai da daidaikun da suke da hannu a lamarin su na nan su na fuskantar tambayoyin jami’an.

 

“Sufeto-janar na ‘yansanda ya bada tabbacin cewa dukkanin wani ko wasu da ke da hannu a lamarin to tabbas za a tuhume shi/su har ma a gurfanar da su kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin da doka ya tanadar,” a cewar FPRO.

 

Idan za a tuna dai Ari ya ayyana cewa Sanata Aisha Binani ce ta lashe zaben gwamnan Jihar amma bai bayyana adadin kuri’un da ta lashe zaben a lokacin ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce. Daga baya kuma INEC ta ce ba a bi ka’ida ba don haka aka soke wannan tare da ayyana gwamna mai ci a jihar, Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

Kodayake Ari ya fito ya ce shi kam ya nan kan bakarsa domin ya yi amfani da tsarin doka ne wajen ayyana Binani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here