Motar da ta kwaso daliban Najeriya daga Sudan ta kama da wuta

0
127

Daya daga cikin motocin bas-bas da suka kwaso ‘yan Nijeriya da suka makale a Khartoum babban birnin kasar Sudan, ta kama da wuta a ranar Litinin.

Daya daga cikin motocin da ta kwaso daliban Nijeriya 50 ta lalace sakamakon fashewar tayar motar.

Dakta Hashim Idris Na’Allah, shugaban kungiyar dattawan daliban Nijeriya da ke karatu a Sudan, yana daya daga cikin fasinjojin motar da ta kama da wutar da ta kwaso dalibai 50, (Maza 49 da mace 1).

Hatsarin ya faru ne da karfe 2:30 na dare agogon kasar Sudan.

Matukin motar dai ya tsaya ne a kusa da shingen bincike na RSF kafin wutar ta fara ci.

Rahotonni sun ce dukkanin daliban sun kubuta cikin tsananin firgici.

An yi kokarin saka ragowar daliban cikin wasu motocin yayin da sauran daliban tare da direban motar suka kwana a shingen bincike na RSF.

Daya daga cikin ‘yan Nijeriya da har yanzu suke Sudan, Sani Aliyu ya bayyana cewar jami’an RST sun taimaka sosai wa daliban har ma suka taimakesu da shayi da safe kafin su bar wajen.

Bayan shan fama dai daliban sun cigaba da tafiya a kokarinsu na ficewa daga Sudan bayan faruwar rikicin da ke cigaba da ruruwa a kasar da ya lakume dumbin dukiya da rayuka.

Sama da ‘yan Nijeriya 1000 ne aka samu nasarar fitar da su daga cikin birnin Sudan ta hanyar Port Sudan bayan shan bakar wahala da suka yi.

‘Yan Nijeriya da suka makale sun shafe tsaron kwanaki biyar a iyar Egypt sakamakon hanasu wucewa da jami’an kasar suka yi domin samun damar shiga jiragen da aka tanadar domin kwasan ‘yan Nijeriyan zuwa nan gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here