Masar ta gindaya tsauraran sharuɗɗa kan kwashe ɗaliban Najeriya ta cikinta

0
144

Masar ta ce za ta yarda a kwashe ɗaliban Najeriya da ke tsere wa faɗan da ake yi a Sudan ta ƙasarta ne kawai idan Najeriyar ta cika wasu tsauraran sharuɗɗa.

Jakadan Najeriya a Masar, Nura Abba Rimi ne ya tabbatar wa BBC da wannan bayanin.

Najeriya dai na da ɗalibai sama da 500 waɗanda suka maƙale a bakin iyakar ƙasar ta Masar, suna jiran izinin shiga domin kwashe su zuwa gida.

A baya ƙasar Habasha ta hana ɗaliban Najeriya bi ta ƙasarta domin tsere wa faɗan na Sudan, wani abu da ya janyo suka daga ɓangarori da dama.

  • Ambasada Nura Abba Rimi ya ce sharuɗɗan da ƙasar ta Masar ta gindaya su ne:
  • Dole sai Najeriya ta bayyana tsarin da ta yi na jiragen da za su sauka a ƙasar domin kwashe ɗaliban.
  • Girman jiragen saman da za su yi jigilar.
  • Tabbatar da cewa za a zarce da ɗaliban kai-tsaye daga bakin iyakar ƙasar zuwa filin jirgi da aka yarje
  • Cikakken jerin sunayen mutanen da za a kwashe ta ƙasar da kuma lambar fasfo ɗinsu na tafiye-tafiye.
  • Cikakkun takardun tafiya.
  • Kasancewar jami’an gwamnatin Najeriya a wuraren kwashe ɗaliban.
  • Da kuma motocin safa da za su kwashi ɗaliban daga bakin iyaka zuwa filin jiragen sama.

ƙasashen duniya dai na ci gaba da rige-rigen ganin sun kwashe ƴan ƙasarsu daga Sudan, bayan ɓallewar faɗa tsakanin dakaru masu mubaya’a ga manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here