Man Utd na son Hakimi, Chelsea kuwa Mane

0
115

Manchester United na son sayen dan bayan Paris St-Germain Achraf Hakimi, dan Morocco mai shekara 24. (Football Insider).

Rahotanni na nuna cewa Chelsea na zawarcin dan gaban Bayern Munich Sadio Mane dan Senegal mai shekara 31, wanda ya koma kungiyar ta Jamus daga Liverpool a bara. (Football London)

Manchester City na shirin gabatar wa tauraron dan gabanta Erling Haaland dan Norway mai shekara 22 sabon kwantiragi. (Football Insider)

Kungiyoyi daban-daban da suka hada da Arsenal da Juventus da Chelsea da kuma Barcelona na nuna sha’awarsu a kan dan gaban Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha, wanda ke shirin barin Selhurst Park. (Telegraph)

Chelsea na da kwarin gwiwa Mason Mount, zai yi watsi da zawarcin da kungiyoyi irin su Bayern Munich da Liverpool ke masa ya sabunta kwantiragin ci gaba da zama a Stamford Bridge. (Football Insider)

An yi wa Arsenal da Bayern Munich tayin dan gaban Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 23, saboda alamu na nuna cewa zaman dan wasan na Serbia a kungiyar ta Italiya ya zo karshe. (Tutto Mercato Web)

Chelsea na daga cikin kungiyoyin Premier da ke sa ido a kan matashin dan wasan gaba na kungiyar Stevenage Makise Evans dan Ingila mai shekara 16. (Sun)

Newcastle United na duba yuwuwar sayen dan gaban Roma da Argentina Paulo Dybala. (Calcio Mercato Web)

Sheffield United za ta tsawaita zaman dan wasanta na gaba Oli McBurnie dan Scotland saboda ta samu nasarar tsallakawa gasar Premier. (Sun)

Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya na sa ido a kan dan bayan Brazil Alex Telles, mai shekara 30, wanda Manchester United ta bayar da shi aro ga Sevilla kuma bisa ga dukkan alamu zai sake hadewa da abokin wasansa a United Cristiano Ronaldo. (AS).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here