Najeriya za ta bincika batun gano sinadarin da ke haddasa cutar daji a taliyar Indomie

0
141

Najeriya na shirin gudanar da wani bincike mai zaman kansa a game da sahihancin rahotannin da ke cewa an samu sinadarin da ke haddasa cutar daji a nau’in taliyar Indomie na ‘Indomie Special Chicken Flavour.

Jaridar ‘Premium Times’ da ake walllafawa  aksar taa ruwaito a Lahadin nan cewa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar, NAFDAC ta  tabbatar da shirin gudanar da bincike a kan wannan rahoto.

Wannan ya biyo bayan matakin kasashen Malaysia da Taiwan na dakatar da samar da wannan nau’in na taliyar Indomie a kasashensu.

Wannan ya biyo bayan gano sinadarin ethylene oxide, wanda aka ce yana haddasa cutar daji wato Cancer, wanda ma’aikatun lafiya na kasashen biyu suka yi a cikin taliyar.

Taliyar Indomie dai ta kasance abinci da ya karade dukkannin sassan Najeriya, inda yara da manya ke ta’ammali da shi a gidajensu a kullayaumin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here