City ta koma ta daya a teburin Premier ta yi kasa da Arsenal

0
119

Manchester City ta je ta doke Fulham 2-1 a Premier League, inda Erling Haaland ya ci kwallo na 50 a dukkan fafatawa a bana.

Minti uku da take leda Erling Haaland ya ci kwallo a bugun fenariti na 50 a kakar nan a karon farko, bayan bajintar Tom Pongo na Aston Villa a 1931.

Haka kuma kwallo na 34 da ya zura a raga a Premier League ya yi kan-kan-kan da Andy Cole a Newcastle a 1993-94 da kuma Alan Shearer a Blackburn a kakar gaba.

Minti 12 da cin kwallon farko mai masaukin baki, Fulham ta farke ta hannun, Carlos Vinicius.

City ta kara na biyu a minti na 36 ta hannun Julian Alvarez, hakan ya ba ta maki ukun da take bukata a karawar.

Da wannan sakamakon City mai kwantan wasa ta koma ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki daya tsakaninta da Arsenal, wadda ta koma ta biyu.

Wannan shine karon farko da City ta hau kan Gunners a kan teburi tun bayan cikin watan Fabrairu – City na fatan lashe Premier League da Champions League da FA Cup a kakar nan.

Wasan farko da City ta buga kenan tun bayan doke Arsenal 3-1 ranar Laraba, wanda hakan ya dora kungiyar a turbar lashe babban kofin tamaula na Ingila na bana, kuma ita ce mai rike da na bara.

Idan har City ta dauki kofin za ta zama ta farko a Ingila da ta lashe biyar daga kaka shida baya kenan.

Kungiyar da Guardiola ke jan ragama ta yi karawa 18 a jere ba tare da an doke ta a dukkan fafatawa.

Saura wasa shida ya rage wa City a Premier League a kakar nan, wadda ke fatan yin nasara a karawa biyar daga ciki.

Wasan gaba da City za ta buga shine da West Ham a Etihad ranar 3 ga watan Mayu, sannan ta kece raini da Leeds United.

Daga nan za ta ziyarci Real Madrid domin buga wasan farko a daf da karshe a Champions League a Santiago Bernabeu ranar 9 ga watan Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here