Mai ƙidaya harbe-harben bindiga a Amurka ya gaji ya daina tuna sunaye

0
83

Mark Bryant, mai sana’ar ƙidaya mutanen da aka harba da bindiga.

Aiki ne da ake yi ba dare ba rana a Amurka – inda fiye da mutum biyu suka mutu sanadin harbin bindiga duk cikin sa’a ɗaya a bara.

Shekara kusan goma kenan yana wannan aiki, a matsayin babban daraktan wata ƙanƙanuwar cibiya da ba ta neman riba ba, mai suna the Gun Violence Archive.

Tana ƙoƙarin bin diddigin duk wani tashin hankali da ya jiɓanci harbin bindiga lokacin da yake wakana a Amurka.

Ga Mista Bryant, shekarun da ya ɗauka yana ƙidaya gawawwaki, suna da nasu illa.

“A lokacin da muka fara wannan, na ga wata yarinya da aka kashe, kuma zan iya tuna sunanta.

Zan iya tuna shekarunta, da birnin da take da kuma abubuwan da suka auku a lokacin harbin. A yanzu, ba zan iya hakan ba,” In ji Mista Bryant.

“An dawo daga rakiyar wannan”.

Mista Bryant ya zanta da BBC News a farkon wannan wata, kwana ɗaya bayan kashe mutum biyar a wani harbin kan mai uwa-da-wabi a wani banki da ke Kentucky.

Kuma mako biyu bayan kashe mutum shida a wani harbin na kan mai uwa-da-wabi a wata makarantar elimantare da ke jihar Tennessee.

A lokacin zantawar, sai ga saƙo ya faɗo wayar Mark Bryant, ana sanar da shi game da wani sabon harbin na kan mai uwa-da-wabi.

Wannan lamarin ya auku ne a wani gidan jana’iza da ke birnin Washington DC – minti 20 bayan kammala sutura ga wani mutumin da aka kashe, sanadin harbin bindiga a watan Maris, kamar yadda ‘yan sanda suka yi bayani daga bisani.

An samu harbe-harben kan mai uwa-da-wabi a ƙalla 170 a Amurka cikin wannan shekara ta 2023 – waɗanda cibiyar Gun Violence Archive ta ce an kashe mutum huɗu ko fiye, ban da ɗan bindigan – a ciki mutane aƙalla 233 ne suka mutu, idan an haɗa da su kansu masu harbin.

Wata alama ce da ke nuni da yawan aukuwar irin wannan lamari a Amurka, kuma mai yiwuwa ne, tuni adadin ya zarce haka a lokacin da aka wallafa wannan labari.

Sai dai harbin kan mai uwa-da-wabi, wani ɗan ƙaramin kaso ne, idan aka kwatanta da illahirin miyagun ayyukan tarzomar bindiga da ke faruwa kullum a Amurka.

Bayani na ranar 26 ga watan Afrilu, yana nuna cewa mutum 13,386 ne suka mutu a tashe-tashen hankulan bindiga a wannan shekara.

Wannan ya haɗa da wata mace ‘yar shekara 20 da aka harbe, bayan ta yi kuskuren shiga wani titin cikin unguwa.

An ji wa ƙarin dubban mutane raunuka, kamar wani matashi ɗan shekara 16 da aka harba da bindiga bayan ya ƙwanƙwasa ƙofar wani gida bisa kuskure.

Mista Bryant, wanda ke bayyana kansa a matsayin ƙwararren mai tara bayanai, ya kafa cibiyar Gun Violence Archive ne a 2013, lokacin da ya gano wani “gagarumin giɓi” wajen samu da kasancewar sabbin alƙaluma na haƙiƙa. Don haka ya miƙe tsaye don yin wani abu game da lamarin.

“Da muka fara aikin, mun ɗauka ba za mu fi shekara biyar ba kawai, amma sai muka ga muna ƙara bunƙasa, muna ta girma, muna ta girma,” Kamar yadda Mista Bryant ya yi bayani.

Haka ma tashe-tashen hankulan bindiga a Amurka.

A tsakanin 2016 zuwa 2021, adadin mace-mace da aka samu daga tashe-tashen hankulan bindiga ya ƙaru da 6,000 kusan kashi 40% kenan.

Adadin ‘yan matasa da aka kashe ko aka jikkata, ya ƙaru da kashi 47%, haka kuma yawan ƙananan yaran da aka kashe ko aka jikkata da bindiga, ya ƙaru da kashi 60%.

Bin diddigin ƙididdigar wannan mummunan lamari, yana shafar rayuwar Mark Bryant, wanda ya ce yana barcin kimanin sa‘a shida ne da daddare, idan ya kwanta da ƙarfe 05:00, yakan tashi da 11:00.

“Na ƙara ƙiba tun lokacin da na fara wannan aiki…Ba na bai wa kaina kyakkyawar kula da ta kamata,” ya ce.

“Matata ta zo ran nan ina tsakiyar barci [a kan kwamfuta] hannuna ɗaya yana kan mawus, ɗayan a kan kibod.”

Mista Bryant ya ci gaba da sa ido a kan alƙaluman tashe-tashen hankulan bindiga a Amurka masu baƙanta rai daga gidansa da ke Kentucky.

Sauran ma‘aikatan cibiyar 24 da aka ɗauka aikin kwanturagi, su ma suna aiki daga nesa kuma sun warwatsu a sassan Amurka.

Domin samar da ingantaccen bayanin duk wani tashin hankali bindiga ba dare ba rana, Mista Bryant ya ce shi da ayarinsa, suna duba majiyoyi guda 3,000 zuwa 4,000 kullum: shafukan intanet na hukumomin tsaro, da kafofin labarai, da soshiyal midiya da ire-irensu.

“A zahiri, ba aiki ne mai wahala ba, amma wahalarsa a tunani take,” in ji shi.

“Zuciyata ta ƙeƙashe. Babu wani abu da ke ba ni mamaki yanzu.”

“Idan na ji wayata ta kaɗa yanzu don sanar da ni cewa an kai harin mai uwa-da-wabi, inda aka harbe mutum 42, abin da zan yi shi ne, to, ai kuwa aikina yau bai ƙare ba.”

Ga wasu ma’aikatansa su ma, ba lamari ne mai sauƙi ba.

“Muna da wasu ma’aikata, kamar sauran mutane, wani ya ga kashe jarirai ya yi yawa, sai ya ce ba zai iya ci gaba da jurewa ba,” in ji Mista Bryant. “A koyaushe ina cikin neman sabbin ma’aikata.”

Wani zai yi tunanin cewa kasancewar ya kwan da zurfin sanin cutarwar da bindigogi ke yi – abu na farko da ya fi sanadin mutuwar ƙananan yara da ‘yan matasa a Amurka, zai sa Mista Bryant zama mai adawa da bindiga. To ba haka ba ne.

Tun yana ɗan shekara biyar ya fara harba bindiga.

Ya koyi harbin bindiga wajen mahaifansa a gabashin Kentucky inda ake taruwa bayan an dawo daga coci ranar Lahadi, a yi ta auna ɓerayen da ke zarya a cikin shara.

“Na mallaki ‘yan bindigogi kamar fistol-fistol da ribolba,” ya ce da yawansu ma gado ya yi.

“Wani kawunka zai mutu, sai matarsa ta zo ta ce ‘karɓi wannan’….da haka na tara wannan abin ba-sabon-ba.”

“Ni ban tsani bindiga ba,” Bryant ya ce. “Wani zai yi tunanin tun da ina yin wannan aiki, to lallai ina ƙin bindigogi ne, amma albishirinku, ina da bindigogi.”

“Abu ɗaya da ban yi ba, ba ni da zungureriyar bindiga.

Ba na zuwa farauta,” ya ce. “Ba na sha’awar ajiye bindigar nan ƙirar AR-15. Ba na sha’awar bindigogin yaƙi.”

Yadda bala’in tashin hankalin bindiga a Amurka ke ƙaruwa, haka ma buƙatar alƙaluman da za a iya dogaro da su, waɗanda aka samo ta sahihan majiyoyi.

Kuma aikin Mista Bryant, na nuna babu wata alama da ke nuna cewa matsalar tana raguwa.

“Na kasa gane me yake damun mutane har suke aikata haka,” Mista Bryant ya ce “Akwai yawan fushi da yawan ƙiyayya.”

Cibiyar archive ta fara aiki ne a matsayin wani aikin bincike don jaridar intanet mai suna Slate, kuma aka ƙaddamar da ita bisa ƙa’ida da taimakon kuɗi daga wani ɗan kasuwa mai burin ganin an inganta tsage gaskiya.

Ta zama wata ƙwaƙƙwarar madogarar tashar BBC News, kuma da yawan manyan kafofin labarai na Amurka, har ma da Kotun Ƙoli – da duk mutumin da ke son fahimtar girman tashe-tashen hankulan bindiga a Amurka.

Kodayake, hukumar binciken manyan laifuka ta FBI da Cibiyoyin Daƙile Yaɗuwar Cutuka duk suna tattara irin waɗannan bayanai, amma ba sa fitar da nasu alƙaluman sai bayan watanni – ko shekaru – da shuɗewar al’amarin.

Idan aka kwatanta, Mista Bryant ya ce cibiyarsu na shigar da bayanai na mafi yawan harbe-harben da aka yi a shafinta na intanet ne cikin sa‘a 72.

“Akwai rashin sanin ciwon kai a batun bindigogi da ke buƙatar a magance, don kada mutane su mutu,” ya ce. “Ina so na dakatar da tashin hankalin.”

Shi kansa haƙiƙanin aikin tattara alƙaluma a kan wani batu maras daɗin ji, mai cike da rarrabuwar kai a siyasance da bisa doron zuciya, kamar tashin hankalin bindiga, ya janyo matsin lamba da bibiyar harkokin cibiyar.

“A wasu lokuta nakan ɓata ran mutanen da ke ɓangaren kare tashe-tashen hankulan bindiga kuma tabbaas a wasu lokuta, nakan ɓata wa masu rajin kare ‘yancin mallakar bindiga.

Sai dai ranar da na fi farin ciki, ita ce lokacin da na wallafa bayanin da dukkansu za su yi fushi da ni,” ya ce.

“Hakan na nuna min cewa ina aikina daidai-wa-daida.”

“Mu namu ƙididdiga ce kawai.

Muna aiki da alƙaluma ne kawai,” Mista Bryant ya ce.

“Muna ci gaba da ƙirgawa kawai. Abin da muke yi kenan – mu ci gaba da ƙirgawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here