Dalilin da ya sa Netflix zai kashe Dala biliyan 2.5 kan fina-finan koriya ta kudu

0
101

Tun a ranar Litinin Shugaban Netflix, Ted Sarandos ya yi wannan albishir bayan wata ganawa da shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol.

Yoon na ziyarar kwanaki shida a Amurka.

“Mun yanke wannan shawara ce saboda muna da kwarin gwiwa cewa dandalin shirya fina-finan Koriya ta Kudu na da labarai masu kayatarwa.” Sarandos ya ce cikin wata sanarwa.

Yoon ya kwatanta wannan sanarwa a matsayin “babbar dama” ga masu kirkirar labarai da dandalin na Netflix.

Fina-finan Koriya da wakokinsu suna samun karbuwa a ‘yan shekarun nan idan aka yi la’akkari da fina-finai irinsu Parasites da mawaka irinsu BTS.

Fim din “Squid Game” da ke ba da labarin yadda aka hada gasa mai cike da hadari tsakanin wasu mutane da bashi ya yi wa katutu, ya zamanto fim da aka fi kallo a shekarar 2021, inda ya samu sama da mutum miliyan 1.6 da suka kalla.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here