Ci-da-zucin ‘yan adawa ne ya kayar da su zaɓe – Buhari

0
98
Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi imani ci-da-zuci ne babban abin da ya janyo taron ‘yan adawar Najeriya suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce.

Ya bayyana haka lokacin da ya karɓi gwamnonin jam’iyyarsa ta APC a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Yana cewa a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki take aiki tuƙuru don ci gaba da mulki a zaɓukan da aka yi a baya-bayan nan, ‘yan adawa suna can sun cika da ci-da-zuci.

“Sun je suna ta faɗa wa masu goya musu baya a ƙasashen waje cewa, sai sun kayar da APC.

Yayin zaɓen na 25 ga watan Fabrairu, ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya smau ƙuri’a 8,794,726.

Sai Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya samu ƙuri’a miliyan 6,984,520.

Ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi yana da ƙuri’a miliyan 6,101,533, yayin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zo na hudu da ƙuri’a miliyan 1,496,687.

Shugaba Buhari ya ce jam’iyyarsu ta yi nasara ne saboda ta haɗa ƙwarin gwiwar da take shi da taka-tsantsan kuma ta yi aiki tuƙuru har ya kai ta ga nasara.

Ya ce yanzu ma ga shi ci-da-zucin yana haifar wa ‘yan adawan ƙarin matsaloli fiye da kowa.

“Abin na yi musu wahala su yi wa masu goyon bayansu na ƙasashen waje gamsasshen bayani a kan abin da ya sa suka gaza kayar da mu,” in ji Buhari.

A cewarsa, sun haɗa ci-da-zuci da ji-ji-da-kai da bahagon lissafi, kuma su ne suka ja musu faɗuwa a zaɓukan bana. “Wannan ya sake haifar da ƙarin matsaloli a cikinsu. ta kai har ana tambaya. Me ya sa suka kasa kayar da mu?”

Shugaba Buhari ya ce babban dalilin da ya sa shi taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murna kan nasarar da ya samu, shi ne ‘yan adawa sun samu goyon baya, kuma masu goyo musu bayan daga ƙasashen waje sun lasa musu zuma a baki.

“Hakan ta sa sun tafi da burin cewa za su ci zaɓe, za su kayar da mu.

Wanne irin kuskure ne wannan?” shugaban ya sake tambaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here